Harin Yelwata: Majalisa Ta ba Mazauna Benue Damar Kare Kansu daga 'Yan Bindiga
- Majalisar Benue ta zargi jami'an tsaro da nuna halin ko-in-kula game da kisan kiyashin da ta ce ake yi wa al'ummomi a sassan jihar
- Majalisar ta bukaci mazauna Benue da su tashi tsaye su kare kawunansu daga hare-haren 'yan bindigar , amma su yi hakan bisa doka
- A yayin zaman majalisar, an bukaci Gwamna Hyacinth Alia ya ayyana makoki na kwanaki uku domin girmama waɗanda aka kashe a Yelwata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue – Majalisar dokokin jihar Benue ta danganta yawaitar kashe-kashe a faɗin ƙasar nan ga halin ko-in-kula da jami'an tsaro ke nunawa wajen magance matsalar.
Ta kuma buƙaci al'ummar jihar da su ci gaba da sa ido tare da kare kansu daga 'yan bindiga a cikin iyakokin doka, domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Source: Facebook
Majalisa na so a ayyana zaman makoki a Benue
Majalisar ta kuma buƙaci Gwamna Hyacinth Alia da ya ayyana makokin kwanaki uku domin girmama waɗanda aka yi wa kisan kiyashi garin Yelwata, tare da aiwatar da dokar hana kiwo a faɗin jihar, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kiran ya biyo bayan wani kudirin gaggawa wanda ke da matuƙar muhimmanci da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Guma 1 ta jihar, Terwase Uche, ya gabatar.
Hon. Uche ya sanar da majalisar a hukumance game da irin barnar da wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka yi a garin Yelwata, da ke karamar hukumar Guma.

Source: Original
"A sako masu zanga-zanga" - Majalisar Benue
Shugaban majalisar dokokin Benue, Aondona Dajoh, ya bayar da umarnin sakin dukkanin matasa da aka kama yayin zanga-zangar da aka yi kwanan nan a faɗin jihar.
Umarnin shugaban majalisar na sakin masu zanga-zangar ya fito ne yayin wani zaman gaggawa na majalisar da aka kira.
An samu ƙaruwar martani tare da suka daga jama'a game da ci gaba da tsare mutanen da suka shiga zanga-zangar nuna adawa tabarbarewar tsaro a sassan jihar.
"Zanga-zanga 'yancin mutane ce" - Majalisar Benue
Jaridar Punch ta rahoto Aondona Dajoh yana cewa:
"Zanga-zangar lumana haƙƙi ne da kundin mulki ya tanadar. Bai kamata a hukunta kowa ba saboda ya yi amfani da 'yancin faɗin albarkacin bakinsa a cikin tsarin dimokuraɗiyya."
Shugaban majalisar ya yi kira ga jami'an tsaro da su mutunta haƙƙin masu zanga-zangar lumana tare da tabbatar da cewa za a gudanar da duk wata mu'amalar jama'a cikin ƙwarewa da taka tsantsan.
Majalisar ta yi alƙawarin gudanar da bincike kan yadda aka kama mutanen da kuma tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa don hana sake faruwar hakan.
Tinubu ya dura Benue kan harin Yelwata
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu, ya isa Makurdi, babban birnin jihar Benue, domin duba barnar da 'yan bindiga suka yi a ƙauyen Yelwata da ke Guma.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a jihar, domin tattaunawa kan hare-haren da suka yi sanadiyar rasa rayukan sama da mutane 200.
Haka kuma, ana da yakinin wannan ganawar za ta samar da hanyoyin magance matsalar tsaro, da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa ga al'ummar jihar Benue.
Asali: Legit.ng

