An Taɓo Trump daga Najeriya, Tsohon Minista Ya Yi Zazzafan Martani kan Yaƙin Iran da Isra'ila
- Femi Fani-Kayode ya caccaki shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump bisa kalaman da ya yi kan jagoran addinin Musulunci na Iran
- Tsohon ministan sufurin jiragen ya zargi Trump da goyon bayan Isra'ila, ƙasar da ya ce ta sha aikata laifuffukan yaƙi amma an gaza hukunta ta
- Fani-Kayode ya gargaɗi Trump da cewa kada ya kuskura ya kashe jagoran addini na Iran domin hakan na iya jawo yaƙin duniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya bukaci Shugaban Amurka, Donald Trump da kada ya jefa duniya cikin rikici kan yaƙin Isra'ila da Iran.
Fani-Kayode, wanda ake kira da FFK a taƙaice ya bayyana hakan ne da yake martani kan barazanar da Trump ya yi wa shugaban addinin Iran cewa sun san inda ya ɓuya.

Kara karanta wannan
Ana batun kashe shi, Shugaban Iran, Khamenei ya yi martani mai zafi bayan barazanar Trump

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa mai zafi da ya wallafa a X, tsohon ministan ya soki kalaman Trump kan rikicin, ya bayyana su a matsayin marasa hankali da ba su da tsari na diplomasiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon minista ya taɓo Donald Trump
Ya zargi Shugaba Trump da cewa yana goyon bayan Isra’ila da masu ra’ayin yaƙi da ke Washington, yana mai bayyana shugaban Amurka da mai neman jawo bala'i.
Fani-Kayode ya ce:
“Kai bala’i ne, ka ci amanar aikinka da kiran da Allah ya maka. Ba ka da gaskiya a zuciya, kai maƙaryaci ne. Masu gaskiya ba su goyon bayan kisan gilla, kisan kare dangi, ko zaluntar marasa ƙarfi.”
Fani-Kayode ya gargaɗi Trump da kada ya kai hari ga Jagoran Addini na Iran ko ya aika dakarun Amurka zuwa ƙasar, yana cewa hakan zai iya tayar da ƙura a Gabas ta Tsakiya wanda ka iya jawo yaƙin duniya.
"Ka kashe Jagoran Addini na Iran idan kana da ƙwarin gwiwa, sannan idan hakan zai birge ka, ka tura sojojin ruwa na Amurka su mamaye ƙasarsa. Wannan zai nuna farkon ƙarshen daular Amurka,”
inji shi.
Isra'ila-Iran: Fani-Kayode ya Trump shawara
FFK ya bayyana cewa a da yana ɗaukar Trump a matsayin gwarzo, amma yanzu ya ba shi kunya saboda abin da ya kira girman kai da wulaƙanci da ya kama shi.
Ya bukace shi da ya saurari muryoyin masu hankali a cikin jam’iyyar Republican kuma ya guji maimaita kura-kuran da gwamnatocin baya na Amurka suka tafka a Gabas ta Tsakiya.
“Abin da nake gani a tattare da kai (Trump) shine girman kai kamar na Icarus wanda zai jawo masa lalacewa. Ka bari Isra’ila ta fuskanci yaƙinta da kanta a wannan karon,”
- Inji Fani-Kayode.
Fani-Kayode ba ya goyon bayan Isra'ila
Tsohon ministan na ɗaya daga cikin masu sukar harin da Isra’ila ke kaiwa a Gaza, yana yawan sukar abin da ya kira kashe rayukan Palasɗinawa da lalata kayan more rayuwa da sunan kare kai.
Ya sha bayyana takaicinsa kan yawan mace-macen fararen hula, musamman mata da yara, tare da zargin Isra’ila da aikata laifukan yaki ba tare da an hukunta ta ba.

Source: Twitter
A cewarsa, hare-haren wanda ke tilasta wa mutane barin gidajensu, ba komai bane face kisan kare dangi.
Ya ce lokaci ya yi da ƙasashen duniya, musamman na Yammacin duniya, za su daina mara wa Isra’ila baya a wannan mamaya mai tsanani kuma su fara ɗaukar mataki bisa doka ta ƙasa da ƙasa.
Najeriya za ta kwaso mutane daga Isra'ila, Iran
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta kwashe 'yan Najeriya da suka makale a Isra'ila da Iran.
Hakan dai na zuwa ne yayin da yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra'ila ke ƙara ta'azzara, ƙasashen na ci gaba da kai wa juna hare-hare.
Ma'aikatar kula da harkokin ƙaashen ƙetare ta Najeriya ta tabbatar da cewa za ta fara ƙoƙarin kwaso ƴan ƙasarta daga Iran da Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

