Sanata Ya Gano Matsalar da Ke Ta'azzara Rashin Tsaro a Najeriya

Sanata Ya Gano Matsalar da Ke Ta'azzara Rashin Tsaro a Najeriya

  • Sanata Seriake Dickson ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a sassa daban-daban na Najeriya
  • Dickson wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma ya bayyana cewa rashin shugabanci mai kyau a ƙananan hukumomi na ƙara rura matsalar tsaro
  • Sanatan ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnan Benue kan hare-haren ta'addanci ƴan bindiga suka kai a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Sanata Seriake Dickson, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa rushewar shugabanci da mulki a matakin ƙananan hukumomi na ƙara tsananta matsalar rashin tsaro a faɗin Najeriya.

Sanata Dickson ya magantu kan rashin tsaro
Sanata Seriake Dickson ya koka kan matsalar rashin tsaro Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Seriake Dickson wanda ya yi shekaru takwas ya na gwamna a Bayelsa ya bayyana wannan ra’ayi ne a ranar Litinin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan kulla sulhu, gwamnatin Katsina ta ja kunnen tubabbun 'yan bindiga

Sanatan ya yi kalaman ne bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, dangane da yawaitar kisan mutane a jihar.

“Ina miƙa ta’aziyya ta gareshi, gwamnati da mutanen kirki na jihar Benue, da kuma iyalan da suka rasa ƴan uwansu a wannan mummunan kisan gilla da aka yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."

- Sanata Seriake Dickson

Sanata Dickson ya magantu kan hare-hare a Benue

Sanatan ya bayyana hare-haren da ake kai wa a jihar Benue da cewa kusan sun kai matakin kisan ƙare dangi.

Dickson ya buƙaci a tura dakarun tsaro na tarayya zuwa Benue da sauran wuraren da ake fama da irin wannan matsala.

Ya yi gargaɗi cewa kashe-kashen sun fara zama ruwan dare kuma gama gari.

“Ba za mu iya zama ƙasa da ake yawan kashe ɗaruruwan ƴan ƙasa kullum-kullum ba."
"Mun fara sabawa da zubar da jini sosai har abin ya daina zama labari. Amma wannan abu ne da ba daidai ba. Yana jefa mu cikin hali na mugunta, rashin doka da oda, da kuma zama ƙasa da ta gaza."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Shugaba Tinubu ya sake samun tagomashi a Arewacin Najeriya

- Sanata Seriake Dickson

Sanatan ya yaba da matakin Shugaba Bola Tinubu na tura jami’an tsaro zuwa jihar Benue, yana mai cewa Gwamna Alia ya tabbatar da hakan a cikin tattaunawar da suka yi.

Sanata Dickson ya buƙacia yi gyara kan kananan hukumomi
Sanata Dickson ya yabawa Shugaba Tinubu kan tura dakaru zuwa Benue Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Twitter

Benue: Sanata Dickson ya buƙaci a yi gyara

Dickson ya jaddada buƙatar gyara lamarin mulki da shugabanci daga matakin ƙananan hukumomi.

“A matakin farko na tsarin siyasar ƙasarmu, wato ƙananan hukumomi akwai giɓi, gibin shugabanci da kuma ƙarancin iya aiwatar da ayyuka, wanda hakan ke da tasiri ga tsaron ƙasa gaba ɗaya."

- Sanata Seriake Dickson

Ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar da aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli wanda ya wajabta bai wa ƙananan hukumomi kason kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan Benue ya faɗi masu kai hare-hare

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue, Hyacinth Iormem Alia, ya bayyana mutanen da ke kai hare-hare a jihar.

Gwamna Alia ya bayyana cewa makiyaya masu ɗauke da bindigu waɗanda ba su da shanu ne ke kai waɗannan hare-haren.

Hakazalika ya bayyana cewa wasu daga cikinsu ba ƴan Najeriya ba ne domin suna shigowa ne daga ƙasar Kamaru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng