Kisan Benue Ya Girgiza Najeriya, Kwankwaso, Pantami, Saraki Sun Yi Magana
- Rahotanni sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 200 a wani mummunan hari da aka kai garin Yelwata da ke karamar hukumar Guma, Jihar Benue
- Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan wadanda suka mutu ‘yan gudun hijira ne da suka tsere daga matsaloli a yankunansu
- Shugabanni da dama sun nuna alhini tare da bukatar hukumomi su dauki matakin da ya dace don kawo karshen kisan gilla wa 'yan Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Wani mummunan hari da ya faru a garin Yelwata na karamar hukumar Guma a Jihar Benue ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 200, lamarin da ya girgiza kasa baki daya.
An kai harin ne da dare, inda maharan suka kona mutane da dama da rai yayin da suka musu kwanton bauna.

Kara karanta wannan
Hare haren makiyaya: Abin da Tinubu ya fadawa gwamnan Benue da suka hadu a Aso Villa

Source: Facebook
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan gillar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Yawancin wadanda aka kashe ‘yan gudun hijira ne da suka bar gidajensu sakamakon rikice-rikicen baya.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro a yankin Benue-Nasarawa da sauran sassan Arewa ta Tsakiya.
Maganar Kwankwaso kan kisan Benue
Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana matukar bakin cikinsa game da harin.
Kwankwaso ya ce:
“Lamari ne mai tayar da hankali a tarihinmu. Ya zama dole Gwamnatin Tarayya da ta Benue su hada kai don kawo mafita ta dindindin kan wannan zubar da jini.
"Dole ne a kama masu hannu a wannan danyen aiki, kuma su fuskanci hukunci.”
Pantami ya yi Allah wadai da kisan Benue
Shahararren malamin addini kuma tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya wallafa a Facebook cewa:
“Muna jajantawa iyalan wadanda aka kashe bisa zalunci a Yelwata da sauran wurare.
"Wadanda suka aikata wannan kisan mugaye ne na hakika.
Dole ne hukumomin da abin ya shafa su tabbatar an kama su kuma a hukunta su. Zalunci a ko ina barazana ne ga adalci a ko'ina.”
Ya kuma roki Allah ya tona asirin masu laifin da duk wanda ke bayansu tare da kawo karshen wannan zalunci.
Saraki ya bukaci magance matsalar Benue
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana abin da ya faru da cewa abin firgici ne da ba za a lamunce shi ba.
Saraki ya wallafa a X cewa:
“Mafi muni, mafi yawan wadanda aka kashe ‘yan gudun hijira ne da suka bar gidajensu.”

Source: Twitter
Ya bukaci a sake nazarin tsare-tsaren tsaro a yankin Benue-Nasarawa da sauran Arewa ta Tsakiya, tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Kara karanta wannan
Benue: yan bindiga sun banka wa gidaje da ƴan gudun hijira wuta, mutane fiye da 200 sun mutu
Matashi ya kashe mahaifiyar shi a Benue
A wani rahoton, kun ji cewa wani matashi ya kashe mahaifiyarsa har lahira bayan mata duka a jihar Benue.
Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin ya samu sabani ne da mahaifiyar shi, inda ya mata duka da wata sanda.
Bincike ya tabbatar da cewa mahaifiyar matashin ta mutu ne yayin da aka kai ta asibiti kuma 'yan sanda sun kama shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
