'Allah Ya Isa': Sheikh Ya Dura kan Tawagar Sanusi II da Aka Ci Mutuncin Aminu Dantata
- Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph ya nuna takaici kan cin mutuncin da aka yi wa Alhaji Aminu Dantata a lokacin bukukuwan Sallah a Kano
- A cikin hudubarsa ta Juma'a, Sheikh Triumph ya soki wasu daga cikin tawagar Sarki Sanusi II da suka zagi dattijon attajirin, har suna buga bindiga
- Malamin ya bayyana Dantata a matsayin dattijo da tarihin Kano ba zai cika ba tare da ambatonsa, yana kiran al'umma da su mutunta dattijai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph ya nuna takaci kan abin da aka yi wa Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Malamin ya bayyana rashin jin dadi kan cin mutunci da aka yi wa attajirin a lokutan bukuwan sallah a jihar Kano.

Source: Facebook
Sheikh ya soki tawagar Sanusi II a Kano
Sheikh Triumph ya bayyana haka a wani bidiyon hudubar Juma'a wanda ya yada a shafinsa na Facebook a jiya Juma'a 13 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, malamin ya soki wasu da ke tawagar Sarki Muhammadu Sanusi II da suka yi wa attajitin rashin albarka.
Ya ce abin takaici ne yadda al'umma ta rasa mutunci da mutunta dattijai da ake ganin girmansu a cikin mutane.
A cewarsa:
"Alhaji Aminu Dantata dattijo ne wanda tarihin Kano ba zai taba cika ba sai ambatonsa ko ambaton gidansa.
"Ko muna so ko ba mu so wannan wata daraja ce Allah ya ba shi amma abin takaici, abin ka yi kuka abin da zai nuna maka muna cikin mafi munin yanayi a wannan gari na mu."

Source: Twitter
Sheikh ya ji zafin abin da yiwa Dantata
Malamin ya nuna takaici kan halayen wasu da kayan sarki da ya kira marasa mutunci, albarka da kuma tarbiyya a lokacin bukukuwan sallah a jihar.
Sheikh Triumph ya bukaci al'umma su riƙa mutunta dattawa irin Aminu Dantata musamman wurin amfani da damar da suke da shi na ilimi na ilimin rayuwa.

Kara karanta wannan
'Kowa ya nemi ƴar garinsu': Rigima ta barke a Borno kan neman aure, an jikkata mutane
Ya ce:
"Wai a ce a wannan sallar wasu marasa albarka marasa tarbiya marasa mutunci kuma wai da kayan sarki su je kofar gidansa suna buga bindiga.
"Ba buga bindigar ba ne, miyagun kalmomin da suke fada, 'A buga ko ya mutu', Inalillahi wa inna ilaihir rajiun.
"Mutumin da ya kai shekara 100 babu kadan, mutumin da duk al'ummar da ta san kanta tattalinsu take yi tana kwasar ilimin rayuwa daga wajensu.
Sheikh Triumph ya magantu kan hawan sallah
Kun ji cewa Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya roki sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya haƙura ya janye hawan sallah da yake shirin yi a jihar.
A wurin tafsirin Ramadan, fitaccen malamin ya bayyana cewa duk mai hankali ya san ba ƙaramar barazana ke tunkaro Kano ba duba da yadda ake gaba da juna.
Sheikh Lawan Triump ya roki ɓangaren Aminu Ado Bayero da su haƙura su janye domin tseratar da jinin al'umma da ceto Kano daga shiga hargitsi.
Asali: Legit.ng
