Tun kafin 2027: Rashin Kudi Ya Hana INEC yin Zaben Cike Gurbin 'Yan Majalisa 7
- Aƙalla guraben kujeru bakwai a Majalisar Tarayya suna nan babu wakilai bayan rasuwar wasu ‘yan majalisa da kuma wasu da suka sauka
- INEC ta ce tana shan wahala wajen gudanar da zaɓen cike-gurbi saboda ƙarancin kuɗi da kuma barazanar tsaro a wasu yankunan Najeriya
- Wasu daga cikin mazauna yankunan da abin ya shafa sun fara korafi kan rashin samun wakilci da walwala a harkokin majalisar tarayya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Hukumar INEC ta bayyana cewa tana shan ƙalubale wajen shirya zaɓen cike gurbi domin maye guraben wasu kujeru a Majalisar Tarayya da suka zama babu wakilai.
Wannan ya biyo bayan rasuwar wasu ‘yan majalisa da kuma saukar wasu daga kujerunsu bayan hawa wasu mukamai a matakin jiha.

Source: Twitter
Wani rahoto da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa duk da ƙorafin da jama’a ke yi, INEC ta ce har yanzu ba ta samu isassun kuɗi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu daga cikin al’ummar da abin ya shafa sun bayyana fargabar cewa rashin wakilci zai iya haifar da matsaloli wajen samar da cigaba da kare muradunsu a matakin ƙasa.
Guraben majalisa da babu kowa a kujerunsu
Rahotanni sun nuna cewa a yanzu akwai kujeru guda bakwai da ba kowa a Majalisar Tarayya, biyu a Majalisar Dattawa, da biyar a Majalisar Wakilai.
Hakan ya faru ne a majalisar dattawa bayan rasuwar Sanata Ifeanyi Uba daga Anambra ta Kudu a watan Satumban 2024.
Sai kuma Sanata Monday Okpebholo daga Edo ta Tsakiya da ya lashe zaɓen gwamna a jihar Edo a watan Satumba 2024.
A Majalisar Wakilai, rasuwar Hon. Isa Dogonyaro daga Jigawa, Hon. Olaide Akinremi daga Oyo, Hon. Ekene Adams daga Kaduna da Hon, Adewunmi Onanuga daga Ogun sun samar da gurabe.
A daya bangaren kuma, Hon. Dennis Idahosa daga jihar Edo ya zama mataimakin gwamna bayan zaben da aka yi a jihar.

Source: Facebook
Rashin kudi ya hana hukumar INEC yin zabe
A wata hira da manema labarai, mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce hukumar za ta shirya zaɓukan cike-gurbi muddin an warware batun kuɗi.
Punch ta wallafa cewa:
“Mun samu cikas saboda ƙarancin kuɗi. Amma muna da tabbacin cewa da zaran an warware matsalar, za mu gudanar da zaɓukan cikin lokaci,”
Jama’a na cigaba da korafi kan rashin wakilci
Yayin da ake jiran INEC ta fitar da jadawalin cike gurbin, wasu mazauna mazabun da ba su da wakilai na cigaba da bayyana damuwa.
Sun bukaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su gaggauta warware matsalar, domin kada hakan ya janyo karancin wakilci da tsaikon ci gaba a mazabunsu.
Legit ta tattauna da Musa Magaji
Legit ta tattauna da Malam Musa Magaji daga karamar hukumar Babura a jihar Jigawa da marigayi Isa Dogonyaro ke wakilta.
Malam Musa ya bayyanawa Legit cewa:
"Lallai bai kamata a ce muna zaune ba mu da wakili a majalisa ba. Ya kamata hukumar INEC ta gaggauta yin zaben.
"Bai kamata a ce rashin kudi ya hana yin zabe ba lura da yadda Allah ya yi wa Najeriya arziki."
INEC za ta yi zabe a Osun da Ekiti
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar da ranakun zaben gwamna a jihohin Osun da Ekiti.
INEC za ta gudanar da zaben gwamna a Ekiti ranar Asabar, 20 ga Yuli, 2026, yayin da na Osun zai gudana ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin rantsar da sababbin kwamishinoni a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


