Gwamnatin Kano Ta Bude Asusun Tallafawa 'Yan Kasuwar Waya da Gobara Ta Cinyewa Kaya

Gwamnatin Kano Ta Bude Asusun Tallafawa 'Yan Kasuwar Waya da Gobara Ta Cinyewa Kaya

  • Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin bincike kan gobarar kasuwar waya da ta lalata dukiyoyin daruruwan ’yan kasuwa
  • Kwamitin zai binciki musabbabin gobarar, tantance barnar da ta faru, tare da bada shawarwari kan hanyoyin dakile faruwar hakan a gaba
  • Gwamnati ta nemi masu hannu da shuni da kungiyoyi su tallafa wa wadanda abin ya shafa ta asusun gwamnati domin a tabbatar da adalci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin bincike domin gano musabbabin gobarar da ta tashi a kasuwar waya da ke Farm Centre, wacce ta kone miliyoyin Naira.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne aka hango hayaki ya turnike rukunin shagunan Dan Sulaika Plaza, inda ya kone kayyaki da dama kurmus kamar gawayi.

Kara karanta wannan

Matar Sanata ta shiga matsala, kotun Ingila na tuhumarta da halasta kudin haram

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano samar da kwamiti kan gobarar Farm Centre Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa gwamnati ta kaddamar da kwamitin ne a ranar Talata ta hannun Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Umar Ibrahim, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kafa kwamiti kan gobarar kasuwar Kano

Solacebase ta wallafa cewa Alhaji Umar Ibrahim ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin yin cikakken bincike kan musabbabin gobarar.

Kwamitin zai kuma tantance yawan asarar da aka yi da kuma gabatar da shawarwari kan yadda za a dakile faruwar makamanciyar gobarar a nan gaba.

Gwamnati na nemowa yan kasuwa taimako a Kano
Gwamnatin Kano ta bukaci kar a siyasantar da batun gobarar kasuwar waya Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A jawabin da ya gabatar yayin taron kaddamarwar, Alhaji Umar Ibrahim ya jaddada bukatar hadin kai wajen taimaka wa wadanda iftila'in ya shafa.

Ya ce:

“Bai kamata a siyasantar da wannan ibtila’i ba. Dukkan gudummawa da taimako dole ne su rika shigowa ta hanyar kwamitin ko kuma ta asusun gwamnati da aka ware domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabawa.”

Gwamnatin Kano ta newa 'yan kasuwa taimako

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Dattawan Arewa sun dira a kan masu tallata Tinubu tun yanzu

Gwamnatin Kano ta bukaci kamfanoni da kungiyoyi da kuma ’yan Najeriya masu kishin kasa da su bayar da gudummawa ta hanyar asusun da aka bude domin tallafa wa ’yan kasuwar farm cente.

Kwamitin, wanda Kwamishinan Harkokin Musamman, Alhaji Nasiru Garo ke jagoranta, ya kunshi wakilai daga hukumomin gwamnati, hukumomin agaji, jami’an tsaro da shugabannin kasuwar.

Alhaji Umar Ibrahim ya ce:

“Mun zabi 'yan kwamitin ne bisa cancanta da wakilcin wadanda abin ya shafa domin tabbatar da an gudanar da aiki cikin kwarewa da gaskiya.”

Daga cikin ayyukan kwamitin har da bincike don gano musabbabin gobarar, tantance girman barnar da rayuka ko dukiya, nazarin yadda aka gudanar da agaji a lokacin gobarar da hanyar kare afkuwar irinta a gaba.

Gobara ta tashi a kasuwar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata gobara ta tashi a safiyar ranar Babbar Sallah, ta shafi shaguna da dama a fitacciyar kasuwar wayoyi ta Farm Centre da ke cikin birnin Kano.

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda hayaki ke tashi daga wani sashe na kasuwar, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a musamman ma ’yan kasuwar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shagalin Sallah, mutane sun tafka asarar biliyoyin Naira a jihar Kano

Wani dan kasuwa mai suna Muhammad Daula, ya ce galibin masu shaguna ba su je kasuwa ba a ranar saboda Sallar Layya, kuma bidiyon da wani ya yada a Facebook ne ya jawo hankalinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng