Gwamna Namadi Ya Yabi Tinubu, Ya Bayyana Yadda Ya Ceto Najeriya
- Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya ƙwararo yabo ga shugaban ƙasa, Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Umar Namadi ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya nuna jarumtaka wajen ɗaukar matakan da waɗanda suka gabace shi suka kasa ɗauka
- Ya nuna cewa matakan da Tinubu ya ɗauka sun taimaka wajen fargaɗo da tattalin arziƙin Najeriya wanda ya kama hanyar durƙushewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Namadi ya yabawa shugaban ƙasan ne kan matakan da ya ɗauka don farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da jaridar Leadership ta yi da shi.
Gwamna Namadi ya yabawa Bola Tinubu
Umar Namadi ya bayyana cewa shekaru biyu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan mulki sun kasance masu amfani, ba kawai ga jama’ar jihar Jigawa ba, har ma da kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
Ya ce dole ne shugaba nagari ya kasance da ƙarfin hali wajen yanke shawarar da ta dace da buƙatun jama’a, musamman idan hakan zai amfanar da su a dogon lokaci.
"A Najeriya, muna buƙatar sauyi daga hanyoyin gargajiya na tafiyar da al’amura domin kawar da tsofaffin manufofi da sauya su da sababbin tsare-tsare masu amfani."
"Samun hakan yana buƙatar shugaba mai ƙarfi da jarumta wanda zai iya jagorantar irin wannan sauyi."
"Muna buƙatar shugaba wanda zai iya ɗaukar matakan da a farko mutane za su kasa fahimta, amma daga bisani su amfana baki ɗaya."
"Wannan ne dai a takaice abin da ya bayyana a cikin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin shekaru biyu da suka wuce."
"Shawarar da ya yanke na cire tallafin fetur da daidaita tsarin canjin kuɗaɗe mataki ne da ya dace da ya kamata a ce an dauka tun da dadewa."
"Sai dai shi ne kaɗai wanda ya samu karfin gwiwar aiwatar da hakan duk da ƙalubalen da ke ciki. Ina da tabbacin cewa wadannan matakai ne da suka ceci Najeriya daga sake faɗawa cikin koma bayan tattalin arziƙi da mummunan rikici."
- Gwamna Umar Namadi
Namadi ya faɗi amfanin cire tallafin fetur
Gwamna Umar Namadi ya kuma bayyana cewa tsarin tallafin man fetur bai amfanar talaka, face wasu mutane ƴan tsiraru.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa da farko, cire tallafin ya janyo cece-kuce, yin zanga-zanga, da kuma tsananin ƙuncin rayuwa, amma a yanzu ya fara haifar da ɗa mai ido.
"A matakin gwamnatin tarayya, kuɗin shiga da ke shiga asusun tarayya da ake rabawa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, sun karu sosai."
"Cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnatin tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi ƙarin damar samun kuɗaɗe don aiwatar da aikace-aikacen da ke kyautata jin dadin jama’a da bunƙasa tattalin arziƙi."
- Gwamna Umar Namadi
Peter Obi ya caccaki shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki salon mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Obi ya bayyana cewa akwai kuskure mai girma kan yadda gwamnatin Tinubu ke aiwatar da wasu daga cikin manyan manufofinta.
Ya bayyana cewa da shi ne shugaban ƙasa, da ya bi wata hanya daban saɓanin wacce Tinubu ya bi wajen cire tallafin man fetur.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
