APC Ta Gyara Kalamanta kan Gargadin Sanata Ndume da Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu
- Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta ja kunnen Sanata Ali Ndume ba duk da kalamansa da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu
- Ta bayyana haka ne bayan jam'iyyar ta fitar da wata sanarwa mai kunshe da kalamai masu kama da barazana kan maganganunsa
- Bala Ibrahim, daraktan yada labaran APC, ya ce duk da ra’ayoyin Ndume na bambanta da nasu, amma babu wanda ya gargade shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ba ta gargadi Sanata Muhammad Ali Ndume ba, bisa kalaman sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A hirar da ya yi a baya-bayan nan, Sanata Ndume ya ce tsirarun mutane na juya gwamnatin Tinubu yadda suka ga dama, sannan baya goyon bayan Shugaban ya sake neman takara.

Source: Facebook
A ganawarsa da BBC, Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim, ya ce wadannan malamai ba su jawo APC ta ja kunnen Sanata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC: "Muna mutunta Sanata Ali Ndume"
Bala Ibrahim ya kara da cewa Sanata Ali Ndume dan jam’iyya ne kuma mutum mai daraja a cikinta, kuma ba yanzu ya fara fadin ra'ayinsa kan mulkin Tinubu ba.
Darakta yada labaran ya kara da cewa duk da cewa sukar gwamnati ya yi, APC ba ta sanya masa takunkumi ba saboda ba ta hana ‘ya’yanta bayyana ra’ayoyinsu ba.
A cewarsa:
"Ni a ganina wannan kalamai na Ndume na baya bayannan kamar kashedi yake yi wa shugaba Tinubu, amma da ake ambato cewa kamar an masa gargadi to babu wanda ya yi masa gargadi."
Sannan babu wanda ya ce zai dauki mataki a kansa, amma kuma jam'iyya na da hanyoyin da ta ke bi wajen ladaftar da duk wani dan jam'iyya da ya aikata ba daidai ba."
Tinubu: Ndume ya kafe kan maganganunsa
A nasa bangaren, Sanata Ali Ndume ya ce bai ga abin da ya fada wanda ya zama ba daidai ba a kan gwamnatin ko neman ya Tinubu ya sake neman takara.

Source: Twitter
Sanata Ndume ya ce:
"Dole ne mu fadi abin da ke damun jama'a, ni ba sukar jam'iyyar APC nake yi ba, na fadi gaskiya ne a waje domin ba a samun ganin shugaban kasa ballantana ka fada masa wadannan abubuwan, duk wata hanya da zan bi don naga shugaba Tinubu na bi ta amma ban samu ganinsa ba."
Ya kuma bayyana cewa ba zai daina fadin gaskiya ba, komai dacinta, ko kuwa hakan zai sa jam’iyya ta kore shi daga APC baki daya.
Fadar shugaban kasa ta caccaki Ndume
A wani labarin, kun ji cewa Fadar shugaban ƙasa ta yi raddi mai zafi ga Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa kan sukar gwamnati.

Kara karanta wannan
'Ndume ba ya iya bakinsa,' Fadar shugaban kasa ta yi zazzafan martani ga Sanatan Borno
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, da ya bayyana haka, ya ce kalaman Sanata Ndume ba su da tushe, kuma bai san abin da yake magana a kai ba.
Ya kara da zargin cewa Ndume ya taba yada labarin ƙarya cewa an kai hari kan tsohon hafsan soji, Janar Tukur Buratai, wanda daga bisani aka tabbatar ba gaskiya ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
