Al'umma Sun Shiga Mummunan Firgici bayan Ƙaramar Girgizar Ƙasa Ta Faru a Najeriya

Al'umma Sun Shiga Mummunan Firgici bayan Ƙaramar Girgizar Ƙasa Ta Faru a Najeriya

  • Fargaba ta mamaye mazauna Igbeti a karamar hukumar Olorunsogo, jihar Oyo, bayan wani ƙaramar girgizar ƙasa da ta auku a ƙarshen mako
  • Gwamnatin Oyo ta ce an fara bincike, kuma ba a samu asarar rai ba, tana tabbatar wa da jama’a cewa babu abin tsoro a lamarin tare da kiran a kwantar da hankula
  • Kwamishinan yada labarai ya ce wasu ƙwararru daga jami’ar Ibadan da hukumar OYSMIDA sun shiga bincike domin kare rayuka da dukiyoyi nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Mazauna Igbeti a jihar Oyo sun shiga fargaba bayan girgizar kasa ta faru a yankin wanda ya rikita al'umma.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Olorunsogo da ke jihar Oyo wanda ya afku a ƙarshen makon da ya gabata.

An yi girgizar kasa a yankin Oyo
Mazauna wani gari a Oyo sun shiga damuwa da aka yi girgizar kasa. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Yadda aka samu karamar girgizar kasa a Oyo

Kara karanta wannan

Bam ya tashi da mutane ana tsaka da shagalin babbar Sallah a jihar Sakkwato

Rahoton Punch ya bayyana cewa girgizar ƙasar ta zo ba zato ba tsammani, inda mutane suka firfito da gudu domin neman mafaka daga barazanar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yawancin gine-gine sun fara jijjiga, lamarin da ya sa mazauna suka fara tunanin barin gidajensu don tsira da lafiyarsu da neman mafaka.

Sai dai gwamnati ta jihar Oyo ta kwantar musu da hankali, tana cewa an ɗauki matakai na gaggawa domin shawo kan lamarin.

Gwamnati ta sanar a jawabin Kwamishinan yada labarai, Prince Dotun Oyelade, cewa an fara bincike na gaggawa dangane da karamar girgizar kasa da ta faru a jihar..

Rokon gwamnatin Oyo bayan girgizar kasar

Gwamnati ta roƙi mazauna su zauna lafiya kuma ka da su firgita yayin da ake ci gaba da duba abubuwan da suka haddasa girgizar.

A cewar Kwamishinan, ƙwararru daga Hukumar Raya Ma'adinan Jihar Oyo (OYSMIDA) ƙarƙashin darakta Biodun Oni sun isa wajen da lamarin ya faru.

Ya ce:

“Girgizar na da alaƙa da yadda dutse ke fashewa saboda canjin zafi da sanyin da ya faru daga Faburairu zuwa Mayu.”
An samu karamar girgizar kasa a Oyo
Al'umma a Oyo sun fuskanci karamar girgizar kasa. Hoto: Legit.
Source: Original

Girgizar kasa: Matakin da gwamnatin jiha ta dauka

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Dattawan Arewa sun dira a kan masu tallata Tinubu tun yanzu

Oyelade ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na aiki tare da masana daga jami’ar Ibadan domin nazarin lamarin da samar da hanyoyin magance shi.

Kwamishina ya bayyana cewa jama’a su kwantar da hankalinsu domin babu wanda ya mutu ko rauni da aka samu a wannan lamari.

Duk da haka, a matsayin kariya, kwamishinan ya shawarci waɗanda ke kusa da dutsen da su bar yankin na ɗan lokaci har sai an magance matsalar.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kare rayukan al’umma, kuma za ta rika sanar da jama’a duk wani ci gaban binciken, Tribune ta ruwaito.

An samu 'yar girgizar kasa a Abuja

Kun ji cewa an samu girgizar kasa tare da kara a wasu unguwanni da ke cikin kwaryar birnin tarayya Abuja na tsawon kwanaki uku a jere.

Majiyoyi sun bayyana cewa mazauna yankin Mpape, P.W Neighbourhood da barikin Mopol 24 sun fuskanci wannan girgizar kasar.

Wannan girgizar dai ba ita ce karon farko da aka taba samu a yankunan Abuja ba, ko a shekarar 2018 sai da FEMA ta gargadi mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.