Uwargidar Abacha Ta Yi Magana kan Zargin Mijinta Ya Wawure Dukiyar Najeriya

Uwargidar Abacha Ta Yi Magana kan Zargin Mijinta Ya Wawure Dukiyar Najeriya

  • Matar marigayi Sani Abacha ta fito ta yi magana kan zargin da ake yi wa mijinta na sace dukiyar Najeriya a lokacin da yake karagar mulki
  • Maryam Abacha ta bayyana cewa da gangan aka riƙa yin mummunar fahimta kan yadda tsohon shugaban ƙasan ya gudanar da harkokin kuɗi
  • An ji Hajiya Maryam Abacha ta bayyana cewa ƴan Najeriya suna da matsala domin su kan yarda da dukkanin abin da aka gaya musu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohuwar uwargidar shugaban ƙasa, Maryam Abacha, ta ƙaryata zargin da aka daɗe ana yi cewa mijinta marigayi Janar Sani Abacha ya wawure dukiyar Najeriya.

Sani Abacha wanda ya kasance shugaban mulkin soja da kuma shugaban rundunar sojojin Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998, ya rasu ne a ranar 8 ga watan Yunin 1998.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a Naja

Maryam Abacha ta kare mijinta
Maryam Abacha ta ce Abacha bai saci kudi ba Hoto: Bauchi Online
Source: Facebook

Maryam Abacha ta bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka watsa a gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi, domin tunawa da cika shekara 27 da rasuwar Abacha.

Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasan ta jaddada cewa kuɗin ba sace su aka yi ba, inda ta ce an yi wa mu’amalar kuɗin da mijinta ya yi mummunar fassara ne da gangan.

Shekaru da dama da suka wuce, gwamnatocin Najeriya daban-daban sun ci gaba da dawo da dubban miliyoyin daloli da aka boye a asusun bankuna a ƙasashen waje, waɗanda aka fi sani da "kuɗaɗen Abacha."

Waɗannan kuɗi da aka dawo da su daga ƙasashen Switzerland, Amurka da Birtaniya, an yi amfani da su wajen shirye-shiryen jin daɗin al'umma.

Maryam Abacha ta kare mijinta

A cikin hirar, Maryam Abacha ta ƙalubalanci waɗanda ke yawan zargin da su gabatar da shaidar da ke nuna hakan.

"Wanene shaida kan kuɗaɗen da aka ɓoye? Wa ya ga sa hannun mijina a kan wasu kuɗaɗe da aka ce an ajiye a waje?"

Kara karanta wannan

"Kisan rashin imani," Magidanci ya halaka matarsa mai tsohon ciki a jihar Neja

"Kuma kuɗin da mijina ya ajiye domin Najeriya, a cikin ƴan watanni sai ga su sun ɓace. Me ya sa ba a maganar wannan?"

- Maryam Sani Abacha

Ta bayyana cewa cigaba da zargin mijinta yana nuna matsalar da ake da ita a cikin al'umma.

"Me ya sa kuke yawan zargin mutum ɗaya? Ko wannan ɓangaranci ne? Ko addini ne? Ko me ke damun ƴan Najeriya?"
"Ina yi wa ƴan Najeriya addu’a. Ina yi wa kowa addu’a. Ina fatan mu samu ƙauna da gaskiya a cikin zukatanmu. Ya kamata mu daina ƙarya da zargin mutane ba bisa hujja ba."

- Maryam Sani Abacha

Maryam Abacha ta kare tsohon shugaban kasa
Maryam Abacha ta soki 'yan Najeriya Hoto: Bauchi Online
Source: UGC

Maryam Abacha ta caccaki ƴan Najeriya

Maryam Abacha ta soki ƴan Najeriya da ke yarda da ikirarin cewa gwamnatoci sun dawo da kuɗaɗen da Abacha ya boye a ƙasashen waje.

"Saboda ƴan Najeriya wawaye ne, suna yarda da komai da aka faɗa musu."
"Babangida bai gina Najeriya shi kaɗai ba. Abacha ma bai gina Najeriya shi kaɗai ba. Abiola da kowa, babu wanda ya fi Najeriya girma. Kowa yana da muhimmanci."

Kara karanta wannan

Ana shirin zaɓe, Gwamna ya yi martani kan zargin ziyartar boka domin neman zarcewa

- Maryam Sani Abacha

Ƴaƴan Abacha sun yi wa IBB martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴaƴan marigayi Sani Abacha sun yi martani kan kalaman da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi a kan mahaifinsu.

Sadiq Sani Abacha ya bayyana cewa tarihi zai nuna cewa mahaifinsu shugaba ne nagari duk da irin sukar da ake yi masa.

Ɗan na Sani Abacha ya bayyana cewa ana yi wa mahaifinsu hassada amma duk da haka tarihi ba zai manta da shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng