Halin da Mahajjatan Najeriya 484 Ke ciki bayan Gobara Ta Kama Otal Ɗinsu a Makkah

Halin da Mahajjatan Najeriya 484 Ke ciki bayan Gobara Ta Kama Otal Ɗinsu a Makkah

  • Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa dukkan mahajjatan Najeriya 484 da ke cikin otal ɗin da gobara ta tashi a Makkah sun tsira da lafiyarsu a kasar
  • Gobarar ta faru ne a otal ɗin Imaratus Sanan da ke kan titin Shari Mansur, inda kamfanonin jiragen yawo shida daga Najeriya suka saukar da mahajjata
  • Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Pakistan ya ziyarci wurin, ya umurci a sauya musu masauki da ɗaukar matakan da suka dace a wurin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makkah, Saudiyya - Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta yi martani bayan gobara ya tashi a wani otal da ke dauke da mahajjata.

Hukumar ta tabbatar cewa dukkan mahajjatan Najeriya 484 da ke cikin otal din a Makkah sun tsira da lafiyarsu, babu asarar rai.

Kara karanta wannan

Hajji ya kare: An saka ranar fara dawo da alhazan Najeriya daga Saudiyya

Gobara ta kama otal din mahajjatan Najeriya
Mahajjatan Najeriya sun tsira bayan tashin gobara a otal. Hoto: NAHCON.
Source: UGC

Yadda gobara ta kama otal din mahajjata

Hakan na cikin wata sanarwa da daraktar watsa labarai ta NAHCON, Fatima Usara ta fitar a yau Asabar, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana (lokacin Saudiyya) a otal ɗin Imaratus Sanan da ke titin Shari Mansur.

An ce a nan ne inda kamfanonin yawon buɗe ido guda shida daga Najeriya suka saukar da mahajjata.

Saurin amsa kiran gaggawa daga jami’an agajin Saudiyya da ma’aikatan otal ya taimaka wajen kashe gobarar.

Sanarwar ta ce:

“NAHCON ta tabbatar cewa dukkan mahajjatan Najeriya 484 da suka shiga gobarar otal da ke titin Shari Mansur a Makkah suna lafiya."
Wasu mahajjata sun tsira da gobara ta tashi a otal
Hukumar NAHCON ta ce mahajjatan Najeriya sun tsira bayan tashin gobara. Hoto: NAHCON.
Source: UGC

Ziyarar Farfesa Abdullahi Pakistan zuwa otal din

Bayan faruwar lamarin, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Pakistan ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Pakistan ya samu rakiyar manyan jami’ai ciki har da Alhaji Aliu Abdulrazak da Darakta Alidu Shutti don tantance lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojin Najeriya suka yi bikin sallah a fagen daga a Borno

Farfesa Usman ya umurci a sauya wurin kwanan dukkan mahajjatan zuwa sababbin otal a Mina, tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayan hukumar.

Ya ce:

“Muna godewa Allah da babu asarar rai a wannan lamari."

Tabbacin da shugaban NAHCON ya ba mahajjata

Farfesa ya kuma tabbatar da cewa NAHCON za ta hada gwiwa da kamfanonin yawon buɗe ido domin taimakawa mahajjata.

An riga an kammala binciken sababbin wuraren kwana, kuma an fara sauya masaukin mahajjatan da abin ya shafa domin kare lafiyarsu, cewar rahoton Premium Times.

NAHCON ta nuna godiya ga saurin daukar mataki daga jami’an Saudiyya da kuma ma’aikatan otal wajen shawo kan lamarin cikin sauki ba tare da samun matsaloli ba.

NAHCON ta gargaɗi mahajjatan Najeriya a Saudiyya

A baya, kun ji cewa hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ja kunnen mahajjatan Najeriya kan zaman da za su yi a ƙasa mai tsarki watau Saudiyya.

NAHCON ta gargaɗi mahajjatan kan ɗaukar abubuwan da suka bata yayin da suka gudanar da ibadah a masallacin Ka'aba da ke kasa mai tsari.

Hukumar NAHCON ta kuma buƙaci mahajjatan da su riƙa shan ruwa sosai saboda irin zafin rana da ake yi a kasar Saudiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.