Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Bukaci Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Tinubu

Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Bukaci Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Tinubu

  • Tsagin ƙungiyar Afenifere ya buƙaci majalisa ta fara shirin tsige Bola Tinubu bisa zargin badakala a kwangilar titin Legas-Calabar
  • Shugaban tsagin ƙungiyar, Oba Oladipo Olaitan, ya zargi shugaba Tinubu da bayar da kwangila ga kamfanin abokin hulɗarsa
  • Amma jam’iyyar APC ta reshen Legas ta mayar da martani, tana mai cewa ƙorafin Afenifere barkwanci da wasan yara kawai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Tsagin ƙungiyar Afenifere ya bukaci Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta fara shirin tsige Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa zargin amfani da matsayinsa don amfanin kansa.

Tsagin kungiyar ya nuna damuwa kan zargin bayar da kwangilar aikin titin Legas-Calabar ba tare da ba jama'a damar neman kwangilar ba.

An fara maganar tsige Bola Tinubu
Afenifere ta bukaci majalisa ta tsige Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Shugaban ɓangaren na Afenifere, Oba Oladipo Olaitan, ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Neman rigima: An kira Dangote 'shugaba' a gaban Bola Tinubu a Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce furucin Tinubu yayin ƙaddamar da wani ɓangare na titin, inda ya ce kamfanin da ke aikin na “abokin gwagwarmayarsa” ne, ya nuna cewa an bayar da kwangilar bisa son rai.

Zargin da Afenifere ke yi wa Bola Tinubu

Oba Olaitan ya ce Tinubu ya bayyana a fili cewa ya bai wa kamfanin abokin hulɗarsa aikin titin, wanda hakan ke nuni da cewa shugaban ya ci amanar kare dukiyar ƙasa.

Shugaban tsagin kungiyar ya ce:

“Abin da Shugaba Tinubu ke yi shi ne gina hanya zuwa Atlantic City da yake mallakinsa ne.
"Ya bayyana cewa kamfanin da ke aikin na abokin gwagwarmayarsa ne. An bayar da wannan kwangila ne a ɓoye, kuma ba a bayyana ta ga jama’a ba,”

Afenifere ta bukaci majalisa ta tsige Tinubu

Olaitan ya zargi majalisa da kasancewa shiru a kan batun, yana mai cewa idan har suna da ’yanci da nagarta, ya kamata su ɗauki mataki nan take.

Kara karanta wannan

"Tsarin Tinubu ya zo da alheri," An ji abin da ya jawo man fetur ya yi araha a Najeriya

Shugaban tsagin kungiyar ta bukaci majalaisa ta fara binciken lamarin da ma fara shirin tsige Bola Tinubu.

The Guardian ta wallafa cewa Olaitan ya ce:

“Idan har Majalisar Dokoki ba ta da hannu a cikin wannan al’amari, su nuna hakan ta hanyar daukar matakin tsige shugaban.”

Ya nuna damuwa kan yadda aka ƙaddamar da 4% na aikin titin, yana mai cewa hakan na nuna cewa gwamnatin na iya barin sauran aikin idan ta kammala sashen da ke kaiwa Eko Atlantic.

APC ta yi martani kan batun tsige Tinubu

Amma a martanin jam’iyyar APC reshen jihar Legas, mai magana da yawunta, Seye Oladejo, ya ce zargin da ake yi wa Shugaba Tinubu ba shi da tushe.

Seye Oladejo ya ce ba wani shaidar cewa akwai hulɗar kasuwanci tsakanin Tinubu da kamfanin Hitech.

Oladejo ya ce kalmar “abokin gwagwarmaya” ba ta nufin abokin kasuwanci, yana mai cewa an fassara maganarsa da gangan cikin mummunan fahimta.

APC ta yi magana kan zancen tsige Tinubu
APC ta yi martani kan zancen tsige Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Sarkin Iwo ya yi wa Bola Tinubu kamfen a Osun

A wani rahoton, kun ji cewa Oba Abdulrasheed Akanbi na Iwo ya nemi 'yan Najeriya su goyi bayan Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

An kaɗa hantar Shugaba Tinubu kan matsalar tsaro, da yiwuwar a kifar da APC a zaben 2027

Oba Abdulrasheed Akanbi ya ce yana da kyau a marawa Bola Tinubu baya domin kammala ayyukan da ya fara.

Legit ta rahoto cewa sarkin ya bayyana haka ne yayin gudanar da bukukuwan babbar sallah a garin Iwo na jihar Osun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng