Allah Sarki: Ƴan Bindiga Sun Yi Ajalin Ƴan Sanda 2, Sun Sace Ɗan Ƙasar Waje
- Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari wurin hakar ma’adinai a Oreke-Oke-Igbo, jihar Kwara, inda suka kashe ’yan sanda biyu
- Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa an kashe ASP Haruna Watsai da sufeta Tukur Ogah da sace wani dan kasar waje ƙasa da mutum daya
- Kakakin rundunar ’yan sanda ya ce kwamishinan ’yan sanda ya sha alwashin ceto waɗanda aka sace tare da cafke waɗanda suka aikata laifin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a ranar Laraba sun kai farmaki wajen hakar ma’adinai da ke Oreke Oke-Igbo a jihar Kwara.
Yayin mummunan harin, an tabbatar da cewa sun kashe ’yan sanda biyu da sace wani dan kasar China.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun hallaka 'yan sanda

Kara karanta wannan
DSS da sojoji sun tarfa yaran 'dan ta'adda, sun aika mayakan Dogo Gide 45 barzahu
An samu rahoto cewa an kashe ASP Haruna Watsai da Sufeta Tukur Ogah daga Abuja, waɗanda ke bakin aiki wajen tsaron wurin, cewar Leadership.
An ƙara bayyana cewa waɗanda suka kai harin sun kuma yi garkuwa da mutum biyu: Dan kasar China mai suna Mr. Sam Xie Wie da Mr. David Adenaiye daga jihar Kogi.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi ya tabbatar da harin, inda ya ce maharan sun tafi da bindigogin jami’an da suka kashe.
“Rundunar ’yan sanda ta jihar Kwara na tabbatar da wannan mummunan hari da garkuwa da mutane da ya faru a ranar 4 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 6:30 na yamma.
“Rahoton da DPO na Oreke ya bayar ya nuna cewa wasu ’yan bindiga sun shiga wurin hakar ma’adinai inda suka kashe ASP Haruna Watsai da Tukur Ogah.
“Wannan harin ya kuma kai ga sace Mr. Sam Xie Wie dan kasar waje, da kuma Mr. David Adenaiye wanda shi ma ma’aikaci ne a wajen hakar."
- Cewar rundunar yan sanda

Source: Original
Abin da kwamishinan 'yan sanda ya ce
Ejire-Adeyemi ya ƙara da cewa kwamishinan ’yan sanda na jihar Kwara, CP Adekimi Ojo ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da alkawarin daukar mataki nan take.
Ya ce:
“An kaddamar da bincike da ayyukan leƙen asiri don ceto wadanda aka sace da kuma kama wadanda suka aikata wannan munanan ayyuka."
Rundunar ta ce suna aiki tare da sauran jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin ƙarfafa tsaro da hana faruwar irin wannan hari a gaba, cewar Vanguard.
Ejire-Adeyemi ya ce za a cigaba da bayyana ci gaban bincike yayin da ake samun ƙarin bayani game da yan bindigar.
'Yan bindiga sun hallaka jama'a da dama
Mun ba ku labarin cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'addanci a jIhar Kwara da ke yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Ƴan bindigan sun hallaka mutum shida a wani hari da suka kai a yankin Ilesja-Baruba inda suka buɗewa mutane wuta.
Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta tabbatar da aukuwar harin, ta ƙara da cewa ta cafke wani mai ba ƴan bindiga bayanai.
Asali: Legit.ng
