Musulmi Za Su Yi Sallah cikin Kwanciyar Hankali, NSCDC Ta Ɗauki Matakai a Faɗin Najeriya
- Hukumar Tsaro ta NSCDC ta ɗauko hanyar tabbatar da tsaron jama'a a lokacin shagulgulan babbar Sallah a faɗin Najeriya
- Kwamandan NSCDC na ƙasa, Dr. Ahmed Abubakar Audi ya ba da umarnin tura dakaru 28,000 don tabbatar da tsaron musulmi da sallah
- Ya ce hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarin da take na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Tsaro da Kare Rayuka da Dukiyoyin Jama'a (NSCDC) ta tura dakarun 28,000 zuwa sassan Najeriya domin tabbatar da tsaro a bikin babbar sallah.
Babban kwamandan NSCDC na kasa, Dr. Ahmed Abubakar Audi shi ne ya ba da umarnin tura jami'an tsaron yayin da idin layya da ke ƙara ƙaratowa a Najeriya.

Source: Twitter
Dr. Ahmed Audi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, CSC Afolabi Babawale, ya fitar, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki NSCDC ta ɗauka da Sallah?
Ya ce dakarun NSCDC da aka tura don ba da tsaro a shagulgulan sallah sun haɗa da jami'an sashen leken asiri, tawagar mata ta musamnan, ƴan CTU, SWAT da sauransu.
Babban kwamandan ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na tsare-tsaren hukumar don tabbatar da an yi babbar sallah cikin zaman lafiya da aminci ba tare da wata matsala ba.
Shugaban NSCDC ya ce jami’an da aka tura za su kare kadarorin gwamnati da na ‘yan ƙasa, tare da tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin mutane daga miyagu da ka iya amfani da lokacin sallah don cutar da jama’a.
Dr. Ahmed Audi ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da ɗaukar matakai don yaƙar ta’addanci, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, lalata kadarori, satar man fetur, barna a tattalin arziki da rikicin manoma da makiyaya.

Kara karanta wannan
Gwamna Bago ya bi sahun ƴan sandan Kano, ya hana hawan Sallah saboda abin da ya faru
NSCDC ta buƙaci haɗin kan jami'an tsaro
A taron tsaro da manyan jami’an hukumar, kwamandojin jihohi da shugabannin sassa, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da jama’a da kuma dabarar aiki da bayanan sirri.
“Babu wata hukuma da ke da cikakken iko ko damar magance matsalolin tsaro ita kaɗai. Dole ne mu yi aiki tare da sauran hukumomi da al’umma don samar da zaman lafiya.
Ina da tabbacin cewa za mu yi bikin Sallah cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya,” in ji shi.

Source: Twitter
Dr. Audi ya kuma bukaci kamfanonin tsaro masu zaman kansu da su taimaka wajen bayar da bayanan sirri a kan lokaci, musamman a lokutan da ake buƙatar ɗaukin gaggawa.
A ƙarshe, kwamandan NSCDC ya mika sakon taya murna ga al’ummar Musulmi a Najeriya da ƙasashen waje bisa zagayowar babbar Sallah, rahoton Punch.
Yan sanda sun hana hawan Sallah a Kano
A wani rahoton, mun kawo maku cewa rundunar ƴan sanda ta haramta hawan sallah kamar yadda ta yi a ƙaramar sallah a jihar Kano.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki
Rundunar ta ce bayanan sirrin da ta samu sun tabbatar da cewa har yanzu akwai masu shirin amfani da hawan sallah su tayar da zaune tsarye.
Ta kuma bukaci iyaye da masu kula da yara su ja kunnen ‘ya’yansu kada su bari su fada hannun masu tada fitina a lokacin Babbar Sallah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
