Bikin Sallah: Matawalle Ya Gwangwaje Mambobin APC a Jihar Zamfara

Bikin Sallah: Matawalle Ya Gwangwaje Mambobin APC a Jihar Zamfara

  • Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi wa mambobin jam'iyyar APC a jihar Zamfara sha tara ta arziƙi
  • Bello Matawalle ya ba da kyautar raguna a gare su domin su yi bukukuwan babbar Sallah cikin walwala
  • Kyautar ragunan da ministan ya yi, za a raba ta ne a dukkanin ƙananan hukumomi 14 da ke faɗin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle, ya yi rabon raguna ga mambobin APC domin bukukuwan Sallah.

Bello Matawalle ya ba da gudunmawar raguna 3,000 ga magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Zamfara domin sauƙaƙa musu bukukuwan Sallah.

Bello Matawalle ya raba raguna ga 'yan APC a Zamfara
Matawalle ya ba mambobin APC raguna a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Source: Original

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Alhaji Tukur Danfulani, ya wakilci Matawalle wajen rabon ragunan a birnin Gusau, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a raba ragunan Matawalle

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bukola Saraki ya fadi lokacin farfadowar jam'iyyar

Alhaji Tukur Danfulani ya bayyana cewa an raba raguna 100 ga kowane ofishin jam'iyyar na ƙarama hukuma cikin ƙananan hukumomi 14 na jihar, rahoton The Sun ya tabbatar.

Wannan ya kai adadin raguna 1,400 da aka ware don ofisoshin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi.

Ya ce waɗannan raguna za a raba su ne tsakanin shugabannin jam’iyya a matakin ƙaramar hukuma, gunduma da kuma rumfunan zaɓe.

Alhaji Yusuf Danfulani ya ƙara da cewa sauran raguna 1,600 an ware su ne domin mata, matasa, dattawa da kuma sauran mutane masu rauni da ke fadin jihar.

Shugaban jam’iyyar ya yaba wa Bello Matawalle bisa wannan kyauta da ya yi, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage wa mutane wahala da matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

Ya ce irin wannan tallafi yana nuna kulawar da manyan ƴan siyasa ke nunawa ga jama’arsu, kuma yana taimaka wa jam’iyyar ta ci gaba da samun goyon bayan al’umma a jihar.

An yabawa shugabannin APC a Zamfara

Haka zalika, Alhaji Yusuf Danfulani ya gode wa sauran manyan shugabannin jam’iyyar a jihar kamar tsohon gwamna, Sanata Abdulaziz Yari da Muktar Idris bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen tallafawa mambobin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda hadakar Atiku, El Rufai za ta iya kawar da Tinubu a 2027', Umar Ardo

Bello Matawalle ya ba da kyauta a Zamfara
Matawalle ya raba raguna a jihar Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Source: Facebook

A ƙarshe, ya yi kira ga jama’ar jihar Zamfara da su ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen yaƙi da ƴan ta’adda da sauran miyagun laifuka.

Ya ce za su hakan ne ta hanyar ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro game da maboyar masu aikata laifuka da dabarunsu.

Ya ce nasarar gwamnati a yaki da rashin tsaro na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.

Matawalle ya caccaki masu sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya soki ƴan siyasar Arewa masu ƙananan maganganu kan gwamnatin Bola Tinubu.

Bello Matawalle ya bayyana cewa ƴan siyasar da ke sukar Shugaba Bola Tinubu, suna yin hakan ne don su yi farin jini a siyasance.

Ministan ya kuma zarge su da ƙoƙarin shafawa shugaban ƙasan baƙin fenti saboda sun kasa samun muƙamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng