Bayan Karrama Bill Gates, an Fadi yadda Ya Hada kai da Dangote Ya Ceci Arewa

Bayan Karrama Bill Gates, an Fadi yadda Ya Hada kai da Dangote Ya Ceci Arewa

  • Shugaba Bola Tinubu ya karrama Bill Gates da lambar CFR saboda gudunmawarsa ga lafiyar jama’a da yaki da talauci
  • Attajirin da abokinsa, Aliko Dangote sun taka muhimmiyar rawa wajen kawar da cutar shan inna a Arewacin Najeriya
  • Bill Gates ya ce zai zuba dukiyar sa gaba ɗaya don inganta lafiya da kawar da zazzabin cizon sauro a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Bill Gates, lambar girmamawa ta CFR a wata liyafa da aka gudanar a Legas ranar Talata.

Tinubu ya bayyana Gates a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Adam da ke ba shugabanni a duniya kwarin gwiwa ta hanyar taimakon talakawa da marasa galihu da ayyukan jin kai.

Bill Gates
Tinubu ya karrama Bill Gates a Legas. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya yi hadaka da tarayyar Turai domin kawo muhimman ayyuka Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lambar CFR tana ɗaya daga cikin manyan lambobin girmamawa da Najeriya ke bayarwa ga waɗanda suka bada gudunmawa wajen ci gaban ƙasa da jin daɗin al’umma.

Bill Gates da Dangote sun ceci Arewacin Najeriya

Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce Gates da Alhaji Aliko Dangote sun zuba fiye da dala biliyan 2 a Najeriya domin inganta lafiya, noma da tattalin arzikin zamani.

A cewarsa:

“Lokacin da Bill Gates ya zo Arewacin Najeriya, akwai matsaloli da rigakafi inda mutane ke ƙin karɓa saboda rashin sani.
"Amma Gates da Dangote sun haɗa gwiwa da sarakunan gargajiya domin wayar da kai.”

Farfesa Pate ya ce wannan hadin gwiwar ce ta taimaka aka kawar da cutar shan inna gaba ɗaya daga Najeriya, musamman a Arewa, inda cutar ta fi kamari a baya.

Tallafin da Bill Gates ya ba Najeriya

Bill Gates ya ce samun wannan girmamawa daga shugaban Najeriya babban alfarma ce gare shi da ƙungiyarsa, inda ya kara da cewa burinsu shi ne inganta lafiyar 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yadda za mu kwace mulki daga hannun Tinubu a 2027,' Atiku, El Rufai sun magantu

Gates ya jaddada cewa Najeriya ta samu nasarori masu tarin yawa a shekaru 25 da suka gabata, musamman wajen rage mace-macen yara.

Ya bayyana cewa Nigeria ce ta fi kowace ƙasa nasara wajen rarraba rigakafin cutar mahaifa (cervical cancer) ga ‘yan mata masu shekaru 9-14.

Bill Gates
Bill Gates ya ji dadin karramawar da aka masa a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Bill Gates zai kawar da zazzabin cizon sauro

Gates ya bayyana wa Shugaba Tinubu cewa gidauniyarsa na da burin kawar da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya cikin shekaru 20 masu zuwa.

The Cable ta rahoto ya ce:

"Za mu ci gaba da yaƙi da rashin abinci mai gina jiki da kuma yaɗa rigakafin da zai kawo ƙarshen zazzabin cizon sauro a Najeriya."

A ƙarshe, ya sha alwashin cewa zai sadaukar da dukiyar sa gaba ɗaya domin tabbatar da cewa Najeriya ta cimma burin ta na ingantaccen tsarin lafiya da kyautata rayuwa.

Gwamna Fubara ya ziyarci Tinubu a Legas

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers da aka dakatar ya kai wa shugaba Bola Tinubu ziyara a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Matashi ya saya wa Tinubu ragon layya, ya yi wa mamar shugaban kasa mai suna

Gwamna Simi Fubara ya kai ziyarar ne yayin da ake rade radin cewa za a iya dawo da shi ofis da kuma sulhu tsakaninsa da Nyesom Wike.

Kwanaki kadan kafin ziyarar, Wike ya fitar da wasu maganganu da suke nuna rashin gamsuwa da matakan sulhu da ake kokarin yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng