Bayan Ya Fice daga PDP zuwa APC, Gwamna Sheriff Ya Shirya Korar Kwamishinoni 3
- Gwamna Sheriff Oborevwori ya gargaɗi kwamishinonin Delta cewa ba zai iya ci gaba da aiki da waɗanda ba sa nuna ƙwazo a cikinsu ba
- Ya karyata jita-jitar sauya mukarrabai, yana mai cewa akwai kwamishinoni biyu ko uku da zai iya sallama saboda ba su aiki yadda ya kamata
- Barazanar korar kwamishinonin na zuwa ne makonni bayan da gwamnan Delta ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya gargaɗi mambobin majalisar zartarwarsa, yana mai cewa waɗanda suka nuna ƙwazo ne kawai za su cigaba da aiki da shi.
Gwamna Sheriff ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da sababbin gine-gine a cikin rukunin gidajen kwamishinoni a Asaba, babban birnin Delta, a ranar Litinin, 2 ga Yuni.

Source: Twitter
Gwamna ya karyata rade-radin sauya mukarrabai

Kara karanta wannan
"Shekara 8 ina matsayin gwamna amma ban samu komai ba," Kalu ya tuna abin da ya faru
Channels TV ta rahoto cewa Gwamna Sheriff ya kuma karyata jita-jitar cewa yana shirin sauya mukarrabansa, sai dai ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci kwamishinonin da ba sa aiki ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Shariff ya ce:
“Idan kana aiki, za ka cigaba da zama. Yanzu haka akwai mutum biyu ko uku da ba sa yin abin da ya kamata. Na faɗa wa ɗaya daga cikinsu yau a coci: 'Ba ka yin aiki yadda ya kamata.'”
Gwamnan ya buƙaci kwamishinoni su zama masu ƙirƙirar sababbin hanyoyin ci gaba, su gabatar da dabarun inganta gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana ganin tasirin ayyukansu.
Gwamnan jihar Delta ya gargadi kwamishinoni
Gwamna Shariff ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kama kwamishinoni da laifi idan ma'aikatarsa ta gaza samar da wani ci gaba.
Hakazalika, gwamnan ya ce zai dora alhakin nasarar da kowacce ma'aikata ta samu a kan kwamishinanta, ba tare da tauye kokarin da kowa ya yi ba.
Jaridar Punch ta rahoto Gwamna Sheriff na cewa:
“Alhakin kwamishinoni ne kula da ma'aikatunsu. Daga yanzu babu wanda zan sake nema a cikin ku. Ku ne ya kamata ku rika zuwa mun da takardunku, ku sanar da ni abin da kuke yi.”

Kara karanta wannan
"Ku bari na nemi zaɓin Allah," Gwamna ya yi magana kan yiwuwar tsayawa takara a 2027
Gwamnan ya kafa misali da wani kwamishina a jihar, wanda ya ce yana yin aiki tuƙuru, kuma dole ne a yaba da yadda yake tafiyar da ma’aikatarsa.

Source: Twitter
Sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Furucin gwamnan na zuwa ne watanni biyu bayan ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, abin da ya janyo rade-radin sauke dukkanin mukarraban gwamnatinsa.
Sheriff ya koma APC tare da tsohon gwamna kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaben 2023, Ifeanyi Okowa.
Haka kuma, dukkanin kwamishinoninsa da manyan jiga-jigan PDP a jihar sun sauya sheƙa tare da shi zuwa jam’iyyar APC mai muki a kasa.
Alkawuran da APC ta yi wa gwamnan Delta
Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC mai mulki ta bayyana farin cikinta bisa sauya sheƙar da Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ya yi zuwa jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce wannan sauyi zai ƙarfafa haɗin kan siyasa a jihar Delta tare da bai wa gwamnatin Bola Tinubu damar cimma manyan manufofinta.
APC ta yi alƙawarin ba Gwamna Oborevwori da sauran da suka sauya sheƙa cikakken goyon baya da haɗin kai da ya dace da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng