Sheikh Jabir Maihula Ya Yi Rashi, Mahaifin Fitaccen Malamin Musuluncin Ya Rasu

Sheikh Jabir Maihula Ya Yi Rashi, Mahaifin Fitaccen Malamin Musuluncin Ya Rasu

  • Kwamishinan harkokin addinai na jihar Sakkwato kuma babban malamin musulunci, Sheikh Jabir Sani Maihula ya yi rashi
  • Allah ya yi wa mahaifin malamin rasuwa yau Talata, 3 ga watan Yuni, 2025 kuma an yi janaza kamar yadda addinin musulunci ya tanada da misalin karfe 4:30 na yamma
  • Manyan malaman musulunci a ciki da wajen jihar Sakkwato sun miƙa sakon ta'aziyya ga Maihula tare da addu'ar Allah Ya jiƙan mahaifinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Mahaifin fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Jabir Sani Maihula ya riga mu gidan gaskiya.

Mahaifin babban malamin na jihar Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya rasu ne yau Talata, 3 ga watan Yuni, 2025.

Sheikh Jabir Maihula.
Allah ya yi wa mahaifin Dr. Jabir Sani Maihula rasuwa Hoto: Dr. Jabir Sani Maihula
Source: Facebook

Sheikh Jabir Maihula ne ya sanar da rasuwar a wani ɗan gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin yau.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Wata mahajjaciya daga Najeriya ta sake rasuwa a asibitin Makkah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi janazar mahaifin Sheikh Jabir Maihula

Dr. Jabir Maihula, wanda shi ne kwamishinan harkokin addinai na jihar Sakkwato ya ce za a yi jana'izar mahaifinsa da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Sanarwar rasuwar ta ce:

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Allah Ya yi wa mahaifin Dr. Jabir Sani Maihula rasuwa. Za a yi Janaza da misalin ƙarfe 4:30 na yamma (yau Litinin) in sha Allah a Runjin Sambo."

Tuni dai malaman addinin musulunci a ciki da wajen jihar Sakkwato suka fara miƙa sakon ta'aziyya da addu'ar Allah ya jiƙan mahaifin kwamishinan.

Dr. Jabir Maihula.
An yi janazar mahaifin Dr. Jabir Maihula Hoto: Dr. Jabir Sani Maihula
Source: Facebook

Manyan malamai sun yi ta'aziyyar wannan rashi

Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya miƙa sakon ta'aziyya ga Dr. Jabir da ƴan uwansa bisa rasuwar mahaifinsu.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Pantami ya ce:

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Muna mika taaziyyar mu zuwa ga Dr Jabir Sani Maihula da sauran yan'uwansa babba da karami da iyaye mata, bisa ga rasuwar mahaifi.

Kara karanta wannan

Hukuncin da kotu ta yanke wa mutumin da aka kama a bidiyo yana kona Alkur'ani

"Muna rokon Allah, Ya sanya Aljannah ce makoma tare da sauran iyayen mu da malaman mu."

Haka nan kuma Sheikh Ibrahim Disina ya tabatar da rasuwar mahaifin Dr. Jabir Maihula tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa.

Malamin ya ce:

"Mutuwa rigar kowa, Allah ya jikan mahaifin Dr Jabir Sani Maihula. Allah Ya kai haske kabarinsa Ya gafarta masa kurakuransa Ya kyautata bayansu Ameen.

Sheikh Ahmad Guruntum ya yi alhinin wannan rashi tare da miƙa sakon ta'aziyya ga Sheikh Jabir da iyalansa bisa rasuwar mahaifinsu.

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Bisa alhini, muna yiwa ɗan uwa Dr. Jabir Sani Maihula ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa.
"Tabbas wannan babban rashi ne da ya shafe mu gabaɗaya. Muna addu'a Allah ya masa rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya sanya dausayin aljannah a kabarinsa.
"Allah ya ba wa iyalin da ya bari haƙurin jure wannan babban rashin da muka yi. Allah ya jiƙan magabatanmu.

- Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum.

Mahaifiyar Shekh Asadus Sunnah ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa mahaifiyar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah ta riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

"Ku bari na nemi zaɓin Allah," Gwamna ya yi magana kan yiwuwar tsayawa takara a 2027

An tabbatar da rasuwar mahaifiyar Sheikh Asadus Sunnah a shafin malamin na kafar sada zumunta kuma tuni aka yi jana'izarta a Kaduna.

Sheikh Musa Asadus Sunnah malamin kungiyar Izalah ne da ya yi shahara a Najeriya da ma kasashen ketare a fagen wa'azi da tafsiri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262