Babbar Sallah: Ana Fama da Tsada a Najeriya, Dabbobi Sun Yi Kwantai a Nijar

Babbar Sallah: Ana Fama da Tsada a Najeriya, Dabbobi Sun Yi Kwantai a Nijar

  • A daidai lokacin da ake shirin bukukuwan babbar sallah, dabbobi sun yi yawa a kasuwar Turaku da ke babban birni na Niamey
  • Masu sayar da dabbobi a Nijar sun koka da cewa babu riba ko ciniki, duk da yawan dabbobin da suka kawo kasuwa a wannan lokaci
  • Gwamnatin Nijar ta hana fitar da dabbobi zuwa ketare domin rage tsadar su, matakin da ya jawo asara ga masu fataucin dabbobi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Niamey, Nijar - Yayin da ake shirin bukukuwan babbar sallah, ana ci gaba da sayan dabbobi domin layya.

A kasuwar Turaku da ke birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar, dabbobi sun yi bojo babu masu saya a halin yanzu.

Yawan dabbobi ya jawo asara a Nijar
Matakin gwamnatin Nijar ya karya farashin dabbobi a kasar. Hoto: Zinder Best, DW Hausa.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin DW Hausa ya wallafa a Facebook a ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun shammaci masallata a ranar sallah, sun yi kisa

Dabbobi sun yi tashin gwauron zabi a Najeriya

Hakan na zuwa ne yayin da a Najeriya ake kokawa game da tsadar dabbobi a fadin kasar baki daya.

Za a gudanar da bikin babbar sallah a ranar Juma'a mai zuwa amma mutane da dama ba su samu damar sayan abin layya ba.

A kasuwannin birnin Abuja, dillalan raguna sun nuna damuwa kan halin da suke ciki duba da yadda abokan hulda ke kaurace musu.

Mafi yawansu sun danganta hakan da matsin tattalin arziki da ake ciki da kuma tashin farashin dabbobin.

Wasu ma'aikata da sauran yan kasa sun ce sun cire rai kan yanka dabba a wannan karo saboda tashin farashin dabbobi.

An rasa masu sayan dabbobi a Nijar
Dabbobi sun yi araha a Nijar ana shirin babbar sallah. Hoto: Legit.
Source: Original

Dabbobi sun yi yawa a kasuwannin Nijar

Sai da a Nijar da ke makwabtaka da Najeriya, an samu akasin haka saboda dabbobi ne a makare babu masu saya.

Wani mai sayar da raguna a kasuwar Turaku, Abdoulkadir Amani ya koka kan rashin ciniki.

Kara karanta wannan

Rigimar sarauta ta ɓarke da dakataccen Sarki ya kutsa fada domin ƙwace kujerarsa

Amani ya ce akwai raguna a zube a kasuwa babu masu saya idan ma an sayar babu wata riba da ake samu mai tsoka.

Ya ce raguna sun yi yawa ma a kasuwa amma masu saya sai kuka suke yi babu kasuwa.

Sai dai masana sun ce hakan bai rasa nasaba da matakan da gwamnatin Nijar ta dauka kan fitar da dabbobi ketare.

Gwamnatin kasar ta haramta fita da dabbobi zuwa ketare saboda dakile tsadarsu yayin da layya ya gabato.

Mafi yawan masu fataucin dabbobi zuwa ketare sun nuna damuwa game da matakin da aka dauka.

Ali Alhaji Ado ya ce yanzu haka rashin fita da dabbobin ya jawo musu asara mai yawan gaske.

Ado ya bayyana damuwa inda ya ce sati uku kenan suna fama babu kasuwa wasu dabbobi sun mutu wasu ko duk sun rame.

Wani ɗan Nijar ta tattauna da Legit Hausa

Muhammad Inusa da ya dawo Najeriya a hutun bukukuwan salla ya ce tabbas dabbobi sun yi araha a ƙasar.

Ya ce:

"Eh haka ne sun yi araha kamar yadda ka sani ana kuka babu kudin siya duk da sauƙin da aka ce suke da shi."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shagalin Sallah, mutane sun tafka asarar biliyoyin Naira a jihar Kano

Inusa ya ce hakan bai rasa nasaba da matakan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka game da cinikayyar dabbobi.

Sarkin Morocco ya hana yin layya

Kun ji cewa yayin da ake cikin wani hali a Morocco, Sarki Muhammad VI ya bukaci marasa karfi a kasar da su dakatar da yin layya.

Basaraken ya ce ya ba da shawarar ne saboda tsadar rayuwa da ake ciki bayan fari da karancin dabbobi sun haddasa tsada.

Sarkin ya ce zai yanka raguna biyu, daya a karan kansa daya kuma na al’umma, yana mai cewa ya yi hakan don bin sunnan Annabi Muhammad (SAW).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.