Najeriya Ta Yi wa Tchiani martani kan Sababbin Zarge Zargen Kitsawa Nijar Ta'addanci

Najeriya Ta Yi wa Tchiani martani kan Sababbin Zarge Zargen Kitsawa Nijar Ta'addanci

  • Shugaban gwamnatin soja na Nijar, Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya da hada kai da Faransa don tayar da zaune tsaye a kasarsa
  • Janar Tchiani ya ce an shirya taron sirri a Abuja domin tsara yadda za a kai makamai da hari kan Nijar ta hannun ’yan ta’adda
  • Najeriya ta musanta zarge-zargen, inda Ministan Labarai da na Harkokin Waje suka ce Najeriya ba ta da tarihin nuna kiyayya ga makwabta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jamhuriyyar Nijar – Shugaban gwamnatin soja na jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya sake zargin Najeriya da hada kai da Faransa da Amurka wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasarsa.

Tchiani ya kuma zargi Najeriya, jamhuriyar Benin, Faransa, Sin, Aljeriya da Amurka da kokarin hana ci gaban Nijar da sauran kasashen da ke cikin kawancen kasashen Sahel.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya raba hanya da Tinubu da Ganduje, ya fice daga jam'iyyar APC

Tchinai
Shugaban sojin Nijar ya sake zargin Najeriya da hana kasarsa zaman lafiya Hoto: Zinder Best/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A cikin jawabin sa na tsawon sa’o’i uku da aka watsa ta gidan talabijin na kasar, Radio-Télévision du Niger (RTN), Tchiani ya ce an gudanar taro a Abuja kan yadda za a kassara Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tchiani na zargin hadin gwiwar sirri a Abuja

Daily Trust ta ruwaito Tchiani ya ce wani dan Najeriya, Mohammed Mohammed da mataimakin tsohon shugaban hukumar leken asirin Najeriya, Abubakar Rufai, da ake kira Shehu Barde ne suka jagoranci taron.

Tchiani ya kara da cewa taron ya hada da jami’an CIA, wasu manyan jami’an Najeriya da kuma ’yan asalin Nijar da ke gudun hijira tun bayan juyin mulkin 26 ga Yuli, 2023.

A cewarsa, manufar wannan taro ita ce samar da makamai ga ’yan ta’adda tare da shirya kai hare-hare kan Nijar.

Tchiani ya ce a watan Janairun 2025, kasashen Benin, Côte d’Ivoire da wasu kasashen yammacin Afrika sun tura wakilai Abuja inda suka tattauna kan dabarunsu na hana ci gaban Nijar.

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Martanin Najeriya kan zargin gwamnatin Nijar

A martanin kasar nan, mai taimaka wa Ministan Harkokin Wajen Najeriya kan harkokin yada labarai, Alkasim Abdulkadir, ya ce Najeriya ta dade tana nuna ’yan uwantaka ga Nijar.

Tinubu
Gwamnatin Najeriya ta ce babu kamshin gaskiya a zargin jamhuriyyar Nijar Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewarsa:

“A matsayinmu na kasa, kuma bisa tarihinmu, Najeriya ba ta da tarihin nuna kiyayya ga makwabtanta.”

Alkasim ya tuna cewa a ranar 16 ga Afrilu, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya gana da takwaransa na Nijar, Bakary Yaou Sangaré, a birnin Niamey.

Ya ce a lokacin ganawar, ministocin biyu sun jaddada kudurinsu na kara inganta dangantaka, musamman a fannin bunkasar tattalin arziki da tsaron yanki.

A nasa bangaren, Ministan Yaɗa Labarai na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce a zargin da shugaban gwamnatin Nijar ke yi babu tushe balle makama.

Ya ce:

“Najeriya na watsi da zarge-zargen da shugaban Jamhuriyar Nijar ya yi, wadanda ba su da wata hujja.”
“Hankalinmu ya ta’allaka ne kan zaman lafiya da tsaron ƙasarmu, makwabtanta da yankin yammacin Afrika baki ɗaya.”

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

Tchiani ya hana kai dabbobi Najeriya

A baya, mun wallafa cewa yayin da bikin babbar sallah ke kara karatowa, gwamnatin soji ta Nijar ta dauki matakin hana fitar da dabbobi zuwa kasashen waje, ciki har da Najeriya.

Wannan mataki na da nufin tabbatar da wadatuwar dabbobi a cikin gida yayin bukukuwan Sallah, la'akari da cewa kaso mai yawa na al'ummar Musulmi dake Nijar a wannan lokaci.

'Yan kasuwa a jihohin Kano da Jigawa sun nuna damuwa kan yiwuwar karancin dabbobi da tashin farashi a lokacin sallah duk da cewa akwai wadanda aka yi kiwonsu a gida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng