"Ba Ruwan Ƴan Bindiga," Gwamna Ya Kawo Karshen Jita Jita, Ya faɗi Wanda Ya Kashe Ƴar Uwarsa
- Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya bayyana gaskiya kan yadda aka kashe ƴar uwarsa, Atsi Kefas a hanyar zuwa Abuja a 2024
- Kefas ya ce wani ɗan sanda da ke gadin ayarin mahaifiyarsa ne ya ɗana bindiga, ya harbi ƴar uwarsa daga kusa-kusa, amma ba ƴan bindiga ba ne
- Galibin mazauna jihar Taraba sun ɗauka ƴan bindiga ne suka faramaki mahaifiyar gwamnan da yar uwarsa da nufin yin garkuwa da su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Dr. Kefas Agbu, ya bayyana yadda 'yar uwarsa, Atsi Kefas, ta rasu, wanda ake zargin ƴan bindiga ne suka harbe ta a titin Wukari-Chinkai.
Gwamna Kefas ya bayyana cewa wani ɗan sanda da ke gadin mahaifiyarsa ne ya kashe ƴar uwarsa a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jalingo a shekarar da ta gabata, 2024.

Kara karanta wannan
Abin ba daɗi: Ministan Tinubu ya bayyana yadda aka kashe mahaifinsa a jihar Kaduna

Source: Twitter
Mai girma gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo, babbar birnin jihar Taraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda aka yi ajalin ƴar uwar Gwamna Kefas
Kefas ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2024 a kan titin Wukari-Chinkai, lokacin da Atsi ke hanyar zuwa Abuja daga Jalingo tare da mahaifiyarsu.
“A bara, ‘yar uwata Atsi tana cikin mota tare da mahaifiyata, ana zaton cewa 'yan bindiga ne suka kai musu hari, amma bincike ya nuna ɗan sanda da ke tare da su ne ya harbe ta,” in ji Gwamna Kefas.
Ya ƙara da cewa an gano guntun kwankon harsashi a jikin Atsi lokacin da likitoci ke kokarin ceton rayuwarta kafin daga bisani ta rasu.
Mutane da dama a jihar Taraba sun yi imanin cewa ‘yan bindiga ne suka kai hari kan motar da ke ɗauke da Atsi da mahaifiyar gwamna, suna kokarin yin garkuwa da su.
Wane mataki aka ɗauka kan ɗan sandan?
“Rayuwa tana da muhimmanci ƙwarai a wurina. Ba zai yiwu ka kashe rai kai tsaye ba, kuma ka sa ran Allah zai yarda da kai.
"‘Yar uwata karama ta mutu ne sakamakon harbin ɗan sanda, kuma suna cikin mota daya,” in ji shi.
Gwamna Kefas ya kuma bayyana cewa jami’in dan sandan da ake zargi na nan ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa domin a tabbatar da adalci, in ji Leadership.

Source: Twitter
Kefas ya nuna damuwa da rikicin Karim-Lamiɗo
A cikin taron, gwamnan ya yi shirun minti daya domin girmama Atsi da kuma fiye da mutane 50 da aka kashe kwanan nan a karamar hukumar Karim-Lamido.
“Muna bukatar zaman lafiya da soyayya a tsakaninmu. Ya kamata mutane su zauna lafiya, su zauna da juna cikin aminci domin ci gaban yankinsu.
"Amma abin takaici wasu sun rungumi rikici wanda ba abin da yake haifarwa sai asarar rayuka," In ji Kefas.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa zai kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin da ya auku a Karim-Lamido da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
Mataimakin gwamnan Taraba ya koma gida
A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin gwamnan Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya dawo Jalingo bayan kusan wata hudu yana jinya a Abuja da kasar Masar.
Dawowar mataimakin gwamnan ta kawo ƙarshen tsawon lokacin da aka yi ba tare da an ji ɗuriyarsa ba, lamarin da ya haddasa kace-nace tsakanin al'umma.
Rahotanni sun nuna cewa Aminu Alkali ya sauka a Filin Jirgin Sama na Danbaba Suntai a Jalingo, a jirgin haya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

