NCGC: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Samu Babban Mukami a Gwamnatin Tinubu

NCGC: Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Samu Babban Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Shugaba Bola Tinubu ya kafa kamfanin ba da lamuni na kasa (NCGC), inda Yakubu Dogara ya zama shugaban kwamitin gudanarwa
  • NCGC zai rage hadarin bayar da bashi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, matasa, mata da masana’antu don inganta tattali
  • Kamfanin zai fara aiki a watan Yulin 2025, tare da goyon bayan Bankin Duniya da hukumomin MOFI, NSIA, BOI da CrediCorp

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kamfanin ba da lamuni na kasa (NCGC) tare da zuba masa jarin farko da ya kai Naira biliyan 100.

Tinubu ya kuma nada tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar kamfanin.

Tinubu ya nada Yakubu Dogara a matsayin shugaban gudanarwar kamfanin NCGC
Tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara tare da Shugaba Bola Tinubu a 2018. Hoto: @YakubDogara
Source: Twitter

Tasirin kamfanin NCGC a Najeriya

Fadar shugaban kasa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, kamar yadda rahoton jaridar The Cable ya nuna.

Kara karanta wannan

2027: Wasu 'yan majalisa sun yi watsi da hadaka, sun goyi bayan tazarcen Tinubu

Gwamnati ta bayyana cewa NCGC wata kamfanin gwamnati ne da zai rage hadarin bayar da lamuni tare da bunkasa damar samun kudi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa.

Kamfanin zai taimaka wajen tallafa wa kananan masana’antu, ‘yan kasuwa, masu sayayya da manyan kamfanoni a fadin kasar nan.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Wannan mataki mai tarihi yana da nasaba da sakon sabuwar shekara na 2025 da shugaban kasa ya gabatar, inda ya sha alwashin bude damarmakin bashi da habaka tattalin arziki mai dorewa.”

Bonaventure Okhaimo ya zama shugaban NCGC

Shugaban kasar ya bayyana cewa wannan shiri zai kara karfin gwiwa a tsarin hada-hadar kudi, ya fadada damar karbar lamuni, musamman ga mata da matasa, sannan ya samar da aikin yi da farfado da masana’antu da inganta rayuwar al’umma.

A cewar sanarwar, Bonaventure Okhaimo ne aka nada a matsayin babban manaja kuma shugaban wannan kamfani.

Kara karanta wannan

2027: Sanatoci sun gano dalilin kara karfin Boko Haram da sauran 'yan ta'adda

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sauran wadanda aka nada sun hada da:

  1. Tinoula Aigwedo
  2. Ezekiel Oseni
  3. Yeside Kazeem

Fadar shugaban kasa ta ce dukkan nade-naden za su fara aiki nan take.

An nada wakilan manyan hukumomi a NCGC

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an nada wasu wakilan manyan hukumomin da ke da ruwa da tsaki a kamfanin NCGC a matsayin mambobin kwamitin gudanarwa ba tare da ikon zartarwa ba.

  1. Wadanda aka nada sun hada da:
  2. Shugaban hukumar zuba jari ta NSIA
  3. Aminu Sadiq Umar, shugaban Bankin Masana'antu
  4. Dr. Olasupo Olusi, shugaban hukumar ba da lamuni ta NCCC
  5. Mr. Uzoma Nwagba
  6. Wakiliya daga ma'aikatar kudi, Mrs. Oluwakemi Owonubi
Shugaba Tinubu ya cika alkawari na kafa sabon kamfanin ba da lamuni na NCGC
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya cika alkawari kan kafa NCGC

An bayyana cewa NCGC zai fara aiki a hukumance a watan Yuli, 2025, da jarin farko na Naira biliyan 100, daga hadakar hukumomi da suka hada da MOFI, NSIA, BOI, da CrediCorp.

Fadar shugaban kasa ta ce kungiyar bankin duniya za ta bayar da goyon bayan fasaha ga kamfanin, tare da amfani da kwarewarta a kasashen da ta taba aiki a cikinsu.

Kara karanta wannan

Bayanin da Bola Tinubu ya yi wa Najeriya bayan cika shekara 2 a kan mulki

Shugaba Tinubu dai ya sha alwashin kafa kamfanin bayar da lamuni kafin karshen zango na biyu na shekarar 2025, kuma ana ganin ya cika alkawarinsa.

Tinubu ya nada shugaban hukumar CrediCorp

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Injiniya Uzoma Nwagba ya zama sabon Manajan Darakta kuma shugaban hukumar ba da lamuni ta Najeriya (CrediCorp), bayan amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An tabbatar da nadin nasa ne a ranar Jumu’a, 5 ga Afrilu, 2024, yayin da shugaban kasa ya bayyana gamsuwa da kwarewar wannan matashi mai shekaru 36.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale (na wancan lokaci), ya ce Nwagba na da cikakkiyar kwarewa da gogewa da za su taimaka wajen tafiyar da aikin hukumar CrediCorp.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com