Gusau: Gwamnatin tarayya za ta ceto masana'antu a Zamfara
- Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin farfado da masana'antar Moribund da ke Zamfara
- Hajiya Abubakar ta bukaci wakilan kungiyar ZACCIMA su tantance kamfanonin da ke da yuwuwar samar da ayyukan yi
- Hajiya Abubakar ta ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki tare da kungiyar don farfado da masana'antun jihar
Gwamnatin tarayya da kungiyar Kasuwanci, Masana'antu, Ma'adinai da Noma na Zamfara (ZACCIMA) sun amince su hada karfin gwiwa don gano da kuma ceto masana'antar Moribund wanda ta ke da yuwuwar samar da ayyukan yi a jihar.
Karamar ministar harkokin Kasuwanci, Ciniki da Zuba Jarurruka, Hajiya Aisha Abubakar ta ba da labarin yayin da ta karbi wakilai daga kungiyar don neman taimakon ministar wajen ceto yawancin masana'antun Moribund da ke fadin jihar daga kalubalen da suke fuskanta.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Hajiya Abubakar ta bukaci wakilan kungiyar su tantance kamfanonin da ke da yuwuwar samar da ayyukan yi, da kuma wadanda ke da damar bunkasa ayyukan tattalin arziki a jihar Zamfara.
Ministar ta tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin tarayya za ta zaba da kuma yi aiki tare da su don farfado da masana'antun.
KU KARANTA: Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin da aka sarrafa a jihar Sokoto
Hajiya Abubakar ta lura da cewa auduga, da kuma wasu nau'ikan kaya aikin gona, shine fifiko ga gwamnatin yanzu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng