Gwamnati Ta Kare Neman Bashin $24bn, Ta Lissafo Jihohi 10 da za Su Amfana

Gwamnati Ta Kare Neman Bashin $24bn, Ta Lissafo Jihohi 10 da za Su Amfana

  • Gwamnatin tarayya ta ce rancen Dala biliyan 24 da ta nemi karbowa daga kasashen waje da cikin gida ba zai kara nauyin bashi kai tsaye ga kasar ba
  • Daraktan hulda da jama'a na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ne ya bayyana haka, inda ya ce a hankali za a rika karbo kudin
  • Ya kuma ce ba gwamnati a matakin tarayya ne kawai za ta ci moriyar bashin ba, har da wasu jihohi 10 a sassa daban daban na Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce shirin karbo rancen da ya kai $24bn ba zai kara nauyin bashi kai tsaye ga Najeriya ba.

Mohammed Manga, Daraktan Hulda da Jama'a na Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar domin kare manufar gwamnati kan batun.

Kara karanta wannan

'Mutum sama da 10,000 aka yiwa kisan gilla a mulkin Tinubu," Amnesty Int'l

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta kare shirinta na karbo rancen $24bn Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito Manga na cewa za a yi amfani da bashin wajen gudanar da mafi yawancin ayyukan ci gaba da za a gudanar a 2024 zuwa 2026.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuma za a rika karbar kudin a a hankali, har na tsawon shekaru biyar zuwa bakwai, kuma kowanne bashi, akwai aikin da za a yi da kudin.

'Ayyuka za a yi da bashin kudin,' Gwamnati

Premium Times ta ce a cewar Manga, ayyukan da za a aiwatar da bashin sun shafi sassa masu muhimmanci na tattalin arzikin kasa, ciki har da gina layukan wutar lantarki.

Sannan za a samar da na’urar ban ruwa don kara samar da abinci, jiragen yaki don inganta tsaro, da kuma hanyoyin jiragen kasa da tituna da wasu ayyukan.

Ya kara da cewa mafi yawan kudin bashin za a samo su ne daga abokan cigaban Najeriya kamar su Bankin duniya, Bankin raya Afrika (AfDB) da Hukumar cigaban Faransa (AFD).

Kara karanta wannan

Jerin wadanda ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya zarce a 2027

Sai kuma Bankin Zuba Jari na Turai (EIB), Hukumar Cigaban Japan (JICA), Bankin Exim na kasar Sin, da Bankin Raya Kasashen Musulmi (IsDB).

Gwamnatin ta ce wadannan hukumomi na bayar da bashi cikin sauki, tare da sharudda masu sauki, sannan za a bayar da lokaci mai tsawo don a biya sannu a hankali.

Jihohin da za su ci gajiyar bashin

Manga ya ce ba iya gwamnatin tarayya ce kadai za ta amfana da kudin da za a ranto ba, har ma da wasu jihohin Abia, Bauchi, Borno, Gombe, Kaduna, Lagos, Neja, Oyo, Sokoto, da Yobe.

Tinubu
Gwamnati ta c jihohi 10 za su amfana da bashin Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Shirin karbar bashi ba yana nufin cewa za a karbi duka kudin nan take ba. A hakikanin gaskiya, kudin da za a karba a kowace shekara na cikin kasafin kudin shekara-shekara."
"A shekarar 2025, an tsara karbar dala biliyan 1.23 na bashi daga ketare, amma har yanzu ba a karba ba, kuma an tsara cewa za a fara karbansa a zango na biyu na shekarar.”

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnati na ci gaba da bin ka'ida wajen karbo bashi ta yadda ba zai gurgunta tattalin arzikin kasa ba.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi magana yayin da aka hana shi shiga Saudiyya aikin Hajji

'Bai dace a karbo aron $24bn ba,' Hakeem

A wani labarin, kun ji Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya soki gwamnatin tarayya, tare da bayyana damuwarsa kan sabon bashi da gwamnatin tarayya ke shirin ciwo wa daga kasashen waje.

Dr, Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana fargabarsa kan yadda ci gaba da karbo bashin waje zai kara jefa kasar cikin matsin tattalin arziki, ganin yadda take fama da kanta a yanzu ma.

A ranar Talata, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya karanta wasikar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika masu na neman a sahale masa ya karbo bashin $24bn.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng