Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna, an Kashe Miyagu a Plateau
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan bindiga yayin wani artabu da suka yi a jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiya
- Sojojin sun fafata da ƴan bindigan ne bayan sun yi musu kwanton ɓauna a Teng da ke ƙaramar hukumar Qua'an Pan
- Jami'an tsaron sun ɗanawa ƴan bindigan tarko ne bayan sun samu bayanan sirri kan shirinsu na kai hare-hare a wasu ƙauyuka a yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Dakarun sojoji sun hallaka wasu ƴan bindiga yayin wani artabu a jihar Plateau.
Dakarun sojojin sun hallaka aƙalla ƴan bindiga uku a ƙauyen Teng da ke ƙaramar hukumar Qua’an-Pan ta jihar Plateau.

Source: Facebook
Sojoji sun yi wa ƴan bindiga kwanton ɓauna
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH), Manjo Samson Zhakom, ya bayyana hakan yayin da yake bayani ga manema labarai a ranar Talata a birnin Jos, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya bayyana cewa sojojin rundunar OPSH tare da na runduna ta uku sun kashe ƴan bindigan ne a cikin dajin da ke kusa da yankin.
Manjo Samson Zhakom ya bayyana cewa an samu nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da alburusai daga hannun ƴan bindigan da aka kashe, kuma an ajiye makaman a hannun dakarun tsaro, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Yadda sojoji suka fafata da ƴan bindiga
“A ranar 27 ga watan Mayu, 2025, wasu mayaƙan ƴan ta’adda da ke kan hanyar kai hari kan wasu ƙauyuka a Plateau sun fuskanci kwanton ɓauna daga dakarun runduna ta uku tare da na Operation Safe Haven, inda aka hallaka uku daga cikinsu."
"Hakan ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna cewa ƴan bindiga na shirin kai hari a ƙauyukan Teng da Kayarda da ke ƙaramar hukumar Qua’an-Pan a safiyar ranar 27 ga watan Mayu, 2025."
“A yayin harin, sojoji da suka yi kwanton ɓauna sun fafata da ƴan bindigan, inda suka kashe uku daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere."
"Dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu, makamai guda huɗu, da harsasai na musamman guda 56 masu milimita 7.62."
“An ajiye makaman da aka kwato a hannun sojoji, kuma ana ci gaba da farautar ƴan ta’addan da suka tsere tare da yunƙurin ƙwato ƙarin makamai."
- Manjo Samson Zhankom

Source: Original
Sojoji sun samu nasara kan ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi gumurzu da mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram a jihar Borno.
Dakarun sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun daƙile yunƙurin kai hari ne da ƴan ta'addan suka yi a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Sojojin waɗanda suka samu goyon baya daga jiragen yaƙin sojojin sama sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 16, tare da ƙwato makamai a yayin artabun da suka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

