NiMET: Za a Zabga Mamakon Ruwan Sama a Kaduna, Nasarawa, Neja da Wasu Jihohi 11

NiMET: Za a Zabga Mamakon Ruwan Sama a Kaduna, Nasarawa, Neja da Wasu Jihohi 11

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai karfi zai zuba daga 28 zuwa 30 ga Mayu a jihohi 14, ciki har da Neja, Bayelsa, Edo da Delta
  • NiMet ta yi gargadin cewa ruwan na iya janyo ambaliya da iska mai karfi, wanda ka iya zama barazana ga ababen hawa da gidaje
  • Jihohin Kudu kamar Bayelsa da Delta sun fara daukar matakan kariya tun yanzu yayin da NiMet ta gargadi mutane kan tafiya a ruwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta sanar da cewa za a zabga mamakon ruwan sama daga ranar Laraba zuwa Juma'a.

Rahoton hasashen yanayi na wannan makon da NiMet ta fitar ya nuna cewa jihohi 14 ne za su fuskanci ruwa mai karfi daga 28 ga Mayu, zuwa 30 ga Mayu, 2025.

Kara karanta wannan

Bayan rufe ofishin PDP, Wike ya fadi babbar matsalar da yake fuskanta a Abuja

Hukumar NiMet ta sanar da jihohi 14 da za a zabga ruwan sama na kwanaki 3
Ana zabga ruwan sama gami da walkiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jihohi 14 da za a zabga ruwa na kwana 3

Jaridar The Nation, ta rahoto cewa jihohin da abin zai shafa sun hada da: Bayelsa, Rivers, wasu sassan Delta, Ondo, da kuma jihar Edo.

Sauran jihohin da za a sheka ruwan su ne: Akwa Ibom, Cross River, Imo, Abia, Kaduna, Nasarawa, Kogi, Neja, sai kuma babban birnin tarayya, Abuja.

NiMet ta bayyana cewa mamakon ruwan saman da ake hasashen za a zabga zai iya jawo ambaliya da kuma hadurran iska mai ƙarfi.

Hukumar ta sanar da ita cewa, idan har hasashenta ya tabbata, to ambaliyar da iska mai karfi na iya haifar da barna ga ababen hawa da gidajen mutane.

Jihohin Kudu sun dauki mataki kan ambaliya

Hukumar ta yi kira ga jama'a da su guji tuki cikin ruwan da ke da karfi ko shiga inda ambaliya ke faruwa saboda hakan na iya rike motoci, ko tafiya da su da sauran hadurra.

Kara karanta wannan

Yadda aka samu 'dan sandan da aka kashe a Kano da hannu a kisan 'barayin kaji' tun 2021

NiMet ta kuma ce akwai yiwuwar wannan ruwa zai iya lalata hanyoyi, rage hangen nesa ga direbobi, wanda hakan ka iya haifar da tsaiko ko cunkoso na ababen hawa.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jihohin Kudancin Najeriya da abin ya shafa, musamman Edo, Delta da Bayelsa, sun fara daukar matakan kariya tun kafin ruwan ya sauka.

A Bayelsa, gwamnatin jiha na ci gaba da share magudanan ruwa domin hana ruwa taruwa da jawo ambaliya, inji rahoton Premium Times.

A Delta kuwa, hukumomi sun ja kunnen jama’a kan shirin tunkarar sauyin yanayi, musamman saboda irin yanayin ƙasa mai saukin ambaliya da suke da shi.

NiMet ta gargadi jama'a kan yin tafiye-tafiye yayin da ake ruwan sama
Shugaban NiMet, Prof. Charles Anosike yana zaga ofisoshin hukumar a Arewa. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

Hukumar NiMet ta gargadi 'yan Najeriya

Tun farkon watan Mayu, NiMet ta yi hasashen za a samu yawan ruwan sama fiye da yadda aka saba a wasu yankuna kamar Legas, Cross River da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai hukumar ta kuma yi hasashen cewa wasu sassan yankin Kudu maso Yamma na iya fuskantar karancin ruwa ko kuma tsaikon ruwan sama.

Hukumar NiMet ta bukaci jama’a su rika bibiyar sababbin bayanai da ka iya fitowa, ta hanyar shafukanta na yanar gizo domin samun shawarwari da matakan kariya da suka dace.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun cinnawa ofishin ƴan sanda wuta, an ji abin da ya faru

Yanayin Najeriya a zamanin nan

Sauyin yanayi na ci gaba da yin tasiri mai tsanani a Najeriya, musamman ta fuskar yawan ruwan sama da ambaliya, karancin ruwa, zafi mai tsanani, da kuma sauyin yanayin noma.

A wasu jihohi, ana samun ruwan sama fiye da kima wanda ke haddasa ambaliya, yayin da a wasu sassan kuma ake fama da fari da rashin isasshen ruwa. Wannan matsala na shafar abinci, kiwon lafiya, da tattalin arziki.

A matsayin mataki na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasa (NiMet) tana taka muhimmiyar rawa wajen bada gargaɗi da rahotanni a kan sauyin yanayi.

NiMet tana fitar da bayanan hasashen ruwan sama, iska da zafin rana a kai a kai domin a sanar da gwamnati da jama’a su dauki matakan kariya.

A lokutan da ake sa ran ruwan sama mai karfi, NiMet kan fitar da gargadi kan yiwuwar ambaliya, yuwuwar iska mai karfi da kuma lalacewar hanyoyi.

Kara karanta wannan

Jerin wadanda ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ya zarce a 2027

Haka kuma, NiMet na hada kai da hukumomin jihohi wajen wayar da kan jama’a da kuma tsara hanyoyin dakile illar sauyin yanayi.

Ma'aikatan NiMet sun shiga yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ma’aikatan hukumar NiMet sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya, inda suka fara zagaye filayen jiragen sama don tabbatar da bin umarnin.

Ma’aikatan sun bayyana cewa suna fama da matsin tattalin arziki, inda da dama daga cikinsu ke karɓar rance domin biyan kuɗin haya da kudin makarantar 'ya'yansu.

Shugaban reshen ƙungiyar ma’aikatan, Paul Ogohi, ya bayyana cewa rayuwar ma’aikatan na cikin haɗari, inda ya ce 70% na fama da hawan jini, yayin da kusan 90% ke fama da matsalolin ido.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com