Awanni da Rufe Hedikwatar PDP, Kotu Ta Sanya a Kamo Mata Darakta a Hukumar FCTA

Awanni da Rufe Hedikwatar PDP, Kotu Ta Sanya a Kamo Mata Darakta a Hukumar FCTA

  • Kotu ta bayar da umarnin kama daraktan FCTA Joseph Eriki da wasu da ake tuhuma da laifuka da dama na zamba da jabun takardu
  • Lauyan gwamnati, David Kaswe ya ce abin bi duk wasu hanyoyi da ya kamata amma wadanda ake tuhuma sun ki bayyana a kotu
  • Gwamnatin tarayya na zargin su da laifuffuka shida ciki har da haɗin baki, shiga filaye ba bisa ka’ida ba, da amfani da takardun bogi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Mai shari’a Suleiman Belgore na babbar kotun tarayya Abuja ya bayar da umarnin kama daraktan bincike da gurfanarwa na hukumar FCTA, Joseph Eriki.

Kotun ta bayar da umarnin cafko mata Eriki tare da wasu mutum goma bayan da suka ki halartar zaman kotun duk da alkawarin da suka yi.

Kara karanta wannan

An gano yadda dan kunar bakin wake ya so kutsawa barikin sojoji a Abuja

Kotu ta ba da umarnin a cafko mata daraktan hukumar FCTA da wasu 10
Babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: UGC

Kotu ta sa a kamo daraktan FCTA da mutum 10

Lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya gabatar da bukatar a gaban kotu a ranar Talata domin tilasta wadanda ake tuhuma su gurfana a gaban kotu, inji rahoton The Guardian.

Lauyan ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da aka yi domin ganin an gurfanar da su a shari’ar mai lamba FCT/HC/CR/87/2025 ya ci tura, duk da sanar da lauyoyinsu da masu tsaya musu beli lokacin binciken ‘yan sanda.

A cewar David Kaswe:

“Mun kira su a wayar tarho, mun sanar da lauyoyinsu da masu tsayawa musu beli a ofishin ‘yan sanda lokacin bincike. Amma har yanzu ba su bayyana a kotu ba."

Ya roƙi kotun da ta ba da sammacin kamo su bisa sashe na 124 na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (ACJA) domin tilasta su gurfana gaban alkalin.

Laifuffukan da ake zargin sun aikata

Mai shari’a Belgore ya yanke hukunci da cewa:

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya taka wa Wike birki a harkokin gudanarwa a Abuja

“Tun da sun samu beli daga ‘yan sanda lokacin bincike, na ba da sammaci na kama su gaba ɗaya domin tilasta gurfanar da su a kotu kan tuhume-tuhume shida da gwamnatin tarayya ta shigar tun ranar 31 ga Fabrairu.”

Vanguard ta rahoto cewa Mai shari’a Belgore ya ɗage shari’ar zuwa ranar 4 ga Yuni domin gurfanar da su a gaban kotu.

Gwamnatin tarayya na zargin su da haɗa baki domin aikata laifi, shiga harabar wasu ba bisa ka’ida ba, da kuma hada takardun bogi.

Sauran laifuffukan sun hada da, amfani da jabun takardu a matsayin na gaskiya, da kuma amfani da ƙarfi wajen hana jami’in gwamnati gudanar da aikinsa.

Kotu a Abuja ta ba da umarnin a kamo mata daraktan FCTA da wasu 10
Kofar shiga cikin babbar birnin tarayya Abuja. Hoto: Abuja City
Source: Twitter

Mutane da kamfanoni 11 da ake tuhuma

Sunayen wadanda ake tuhuma da Daraktan su ne:

  1. Boniface Agwu
  2. Ikechukwu Kanu
  3. Donatec Electrical Company Ltd.
  4. Super Structure Ltd.
  5. Weather Field Engineering
  6. Marine Service Ltd.
  7. Asher Information Services Ltd.
  8. Isaac Omoluwa
  9. Nwaimoneye Onyisi
  10. Sarajo Aliyu
  11. Ogbole Michael

Kotu ta sa a kama kwamishinan Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babbar kotun Kano ta bayar da umarnin kama tsohon Antoni-Janar kuma Kwamishinan Shari'a na jihar, M.A. Lawal

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Wike sun dura hedikwatar PDP, sun garkame ofishin jam'iyyar da kwado

Tsohon kwamishinan yana fuskantar tuhume-tuhume huɗu da suka shafi cin amana da ɓatar da Naira miliyan 240, inda aka aika masa da sammaci, amma ya ki zuwa kotun.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ce ta bayar da umarnin cafke M. A. Lawal, tare da ɗage sauraron karar domin ba 'yan sanda damar kamo wanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com