Miyagun Mahara Sun Yi Ta'asa bayan Kai wani Hari a Plateau
- An samu asarar rayuka bayan wasu mahara sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau da ke fuskantar matsalar tsaro a yau
- Harin da aka kai a ƙauyen Mushere da ke ƙaramar hukumar Bokkos ya yi sanadiyyar rasa rayukan akalla mutum bakwai
- Majiyoyi sun bayyana cewa an kai harin ne biyo bayan wasu hare-hare da aka kai a ƙauyen a cikin ƴan kwanakin bayan nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Mahara sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a wani sabon hari da suka kai a jihar Plateau.
Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin da aka kai a ƙauyen Mushere da ke cikin ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin ya faru ne da daren Talata, bayan wasu hare-hare da suka wakana a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahara sun yi ɓarna a Plateau
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa harin ya auku ne sakamakon yunƙurin sace wani mutum da kisan wani fasto da kuma wani hari da aka kai wa wata rugar Fulani.
Wani matashi mai suna Dafang, wanda ke daga cikin shugabannin matasan yankin, ya ce bayan harin farko, mutanen yankin sun fito domin binne waɗanda suka rasa rayukansu.
Sai dai ya ce maharan sun sake kawo wani hari a lokacin da ake shirin jana'iza, wanda hakan ya sa mutane suka riƙa gudu suna neman mafaka.
Ya ce nan take aka tuntuɓi jami’an tsaro, inda suka tura tawagar jami’ai zuwa yankin domin shawo kan lamarin.
“Mutane sun fito domin gudanar da jana’iza, amma kafin su kammala, sai wasu mahara suka sake bayyana suka buɗe wuta, lamarin da ya haifar da rikici da ruɗani. Har yanzu akwai fargaba a tsakanin mazauna yankin."
- Dafang
Me ƴan sanda suka ce kan harin?
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Plateau, ASP Alfred Alabo, ya ce har yanzu ba a kawo masa cikakken bayani ba game da harin, amma yana ƙoƙarin tattara bayanai domin bayyana gaskiyar lamarin.
Sai dai, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, kakakin ƴan sandan bai yi hakan ba.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan hare-hare a Plateau
- An kashe shanu sama da 100 a sabon harin Filato, Fulani sun fadi wanda suke zargi
- 'Yan bindiga sun tarwatsa kasuwa a Filato, sun sace mutane da kayayyaki
- 'Yan bindiga sun kai hari mai zafi Filato, sun afkawa mutane suna barci
Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai harin ta'addanci a.jihar Plateau.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ƙauyen Wereng Camp da ke ƙaramar hukumar Riyom sun hallaka aƙalla mutane takwas.
Miyagun sun ƙona gidaje da dama tare da kwashe kayan abinci daga cikin gidajen da suka lalata na mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

