Boko Haram Ta Ji Dadin Farmakin Sansanin Sojoji, Ta Sake Kai Hari Borno
- Dakarun Operation Hadin Kai sun toshe harin da Boko Haram da ISWAP suka kai a Sabon Marte, tare da kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan
- Rundunar sojin sama ta Najeriya ta taimakawa dakarun da hare-hare ta sama, inda aka yi nasarar fatattakar yan ta'addan da suka so yin barna
- Duk da nasarar da aka samu, sojoji biyu sun riga mu gidan gaskiya, kuma an samu nasarar lalata motar yaki guda da sauran kayayyaki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Dakarun sojojin Najeriya tare da taimakon sashen rundunar sojin sama da ke aiki a karkashin Operation Hadin Kai (OPHK), sun dakile fatattaki yan Boko Haram.
Lamarin ya afku ne a lokacin da yan 'yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka shirya kai wa Marte, makonni kadan bayan ta kai irin wannan hari jihar Borno.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya ce ya samu bayanan sirri da ya tabbatar da harin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, inda aka kai harin da misalin karfe 1.35 na dare a ranar Talata, 27 ga Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram sun kai hari Borno
Rahoton ya bayyana cewa wasu 'yan ta’adda da ba a tantance adadinsu ba sun farmaki sansanin dakarun rundunar da ke Sabon Marte a jihar Borno.
Sai dai da taimakon karin sojoji daga sansanin da kuma dakarun musamman na sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa tare da fafatawa da ‘yan ta’addan.

Source: Facebook
A cewar rahoton, bangaren rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai sun bayar da goyon baya a hare-hare ta sama, wanda ya taimaka matuka wajen tarwatsawa da hallaka 'yan ta'addan.
Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun samu nasarar dakile harin tare da samun cikakken iko da yankin da harin ya faru.
An fara farautar yan Boko Haram
Haka kuma, an fara farautar yan Boko Haram da ISWAP da suka tsere a yayin harin, inda ake kokarin cafke su, yayin da ake tattara makamai da kayan aikin da suka bari.
Sai dai sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabun, sannan an lalata wata motar yaki da dakarun ke amfani da ita.
Harin Sabon Marte ya zo ne a daidai lokacin da dakarun Najeriya ke ci gaba da kai farmaki a yankin tafkin Chadi da arewacin Borno, inda ‘yan ISWAP da Boko Haram ke kokarin kafa sabbin maboyarsu.
Gwamnati za ta yaki Boko Haram
A baya, mun wallafa cewa gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ce ba zai taba amincewa da barin ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya su mamaye kowace karamar hukuma a jiharsa ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan matsalolin tsaro da ke addabar Arewa maso Gabas.
Gwamna Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta taba sassauta matakin da take dauka na yaki da 'yan ta'adda da suke neman mamaye wasu garuruwa a jiharsa ta Borno ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

