Abuja Ta Ɗauki Zafi, Jami'an Gwamnati Sun Kusa ba Hammata Iska a Wurin Rufe Ofishin FIRS
- Hukumar FCTA ta rufe ofishin hukumar tara haraji (FIRS), bankin Access da wani gidan mai a Abuja kan rashin biyan harajin filaye
- Rahoto ya nuna cewa masu gadin FIRS sun yi wa jami'an FCTA turjiya da farko, amma daga bisani an bari sun garƙame ofishin yau Litinin
- Wannan mataki wani yunkuri ne na tilastawa masu filayen biyan harajin ƙasa da ake bin su bashi tsawon shekaru
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya (FCTA) ta fara aiwatar da matakin ladabtarwa ta hanyar rufe wurare masu muhimmanci a Abuja.
FCTA ta garƙame ofishin Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da ke Zone 5, wani reshen Bankin Access, da kuma Gidan Mai na Total da ke Wuse, saboda kin biyan harajin ƙasa na tsawon shekaru da dama.

Source: Twitter
Meyasa FCTA ta rufe ofishin FIRS?
Rahoton Leadership ya nuna cewa FIRS ta gaza biyan harajin kasa tsawon shekaru 25, ne ya sa FCTA ta soke ikon mallakar filin, sannan ta rufe ofishin hukumar da ke Zone 5.
Haka kuma, an rufe wani reshen Bankin Access da ke Wuse da kuma Gidan Mai na Total da ke kusa da shi, sakamakon rashin biyan harajin kasa tsawon shekaru 34.
A cikin wata wasika mai kwanan wata 13 ga Maris, 2025, wacce Daraktan Kula da Filaye na FCTA, Chijioke Nwankwoeze, ya sanya wa hannu, ta ce asalin filin ba na bankin Access ba ne.
Sanarwar ta bayyana cewa filin da Bankin Access ɗin ke amfani da shi kamfanin Rana Tahir Furniture Nigeria Ltd aka bai wa tun usuli, ba wa bankin kai tsaye ba.
Sanarwar ta ce:
“Ministan Birnin Tarayya, bisa karfin ikon da dokar amfani da kasa ta ba shi, ya soke duk wata dama da ikon mallaka da kuke da shi akan filin mai lamba, No. 2456 da ke Wuse, a Abuja.”

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Yadda wani babban malami ya rasu ana tsaka da ruwan sama a jihar Neja
Jami'an FCTA sun gamu da cikas a FIRS
Channels tv ta ce jami’an FCTA da ma’aikatan FIRS sun yi arangama a lokacin da aka je rufe ofishin hukumar a Zone 5.
An ce jami’an tsaron FIRS sun hana FCTA shiga harabar ginin, sai bayan dan lokaci ne aka basu damar shiga, kuma suka kulle ofishin.

Source: Twitter
FCTA ta bayyana cewa wannan mataki yana cikin wani yunkurin na tilastawa masu kadarori sama da 4,700 domin su biya bashin da ake binsu.
Hukumar FCTA ta bukaci duk masu kadarorin da ake bin bashin harajin kasa su gaggauta biya domin kaucewa rasa filayensu.
Dalilin rufe hedikwatar jam'iyyar PDP
A gefe guda, Daily Post ta kawo rahoto hukumar FCTA ta rufe hedikwatar jam'iyyar hamayya ta PDP da ke unguwar Zone 5 a Abuja.
Hadimin ministan, Lere Olayinka ya sanar da cewa Sanata Samaila Mamman Kurfi bai biya haraji na tsawon shekaru 28 ba.
Wike ya ce Tinubu ya kawo canji a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana irin ayyukan raya ƙasa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a Abuja bayan hawansa mulki.
Ministan harkokin Abuja ya ce makaho ne zai ce ba a samu canji mai amfani a babban birnin tarayya ba daga watan Mayun 2023 zuwa yau.
Wike ya ce an tanadi ayyuka. da yawa waɗanda suka haɗa da gina sababbin tituna da gayara tsofaffo da za a kaddamar a bikin cika shekara biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

