Kano: Kotun Shari'a Ta Yi Hukunci, Za a Kashe Matashin da Ya Babbake Masallata
- Kotu ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kona masallata a Kano, inda mutane suka mutu
- Mai Shari'a Halhalatun Huza’i Zakariya ya tabbatar da laifin da ake zargin matashin da shi na kashe masallatan a watan Mayu, 2024
- Baya ga hukuncin kisa, kotun ta kara da wasu hukunce-hukunce guda biyu, wanda ya kawo karshen shari'ar da ake yi da matashin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta rataye shi bisa laifin kone masallata a Gadan, karamar hukumar Gezawa ta jihar.
Lamarin ya faru ne a lokacin da jama'a ke sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024, inda ya zazzaga masu fetur sannan ya cinna masu wuta.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutune da dama sun mutu nan take yayin da wasu aka samu karin wadanda suka rasu yayin da ake yi musu magani a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad.
Kotu ta saurari shari’ar Shafiu Abubakar a Kano
Daily Post ta ruwaito cewa a lokacin da aka gurfanar da Shafiu a kotu a ranar Litinin, alkalin da ke shari’ar, Halhalatun Huza’i Zakariya, ta same shi da laifuffukan da ake zargin ya aikata.
Tuhumomin sun haɗa da kisan kai da gangan, yunƙurin kashe jama'a, haddasa raunuka masu tsanani da kuma kone-kone da gangan.

Source: Facebook
Kotun ta ce laifuffukan sun saba wa sashe na 143, 148 da 370 na dokar Shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta shekarar 2000.
Kotun ta kuma umarci a yi masa bulala guda 100 da tare da cin tararsa ta N1500 bisa mugun laifin da ya aikata.
Kano: Sauran hukuncin da kotu ta yanke
Har ila yau, kotun ta umarci da a kwace baburin matashin, inda za a miƙa wa gwamnatin jihar Kano domin a yi amfani da kudin wajen gyara masallacin da ya kone.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Abubakar a kotu ranar 25 ga Mayu, 2024, inda ya amsa laifin kisa a cikin tuhume-tuhumen guda uku da suka haifar da mutane dama.
An gabatar da sabon tuhume-tuhume guda hudu a kansa ranar 4 ga Yuli, 2024 bayan an samu karuwar wadanda suka rasu.
Jami’ai sun gabatar da shaidu guda bakwai, ciki har da Abdulaziz Yahya, shugaban garin Gadan, da ASP Abdullahi Sajoh Adamawa, jami’in ‘yan sanda da ke aikin rundunar ‘yan sanda ta Gezawa.
An cafke wasu matasa a Kano
A baya, mun ruwaito cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta cafke wasu matasa da yara tare da su yayin da suke daukar wani bidiyo a kusa da gidan gwamnatin duk da haramcin haka.
Wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafen da al’umma ke yi kan yadda matasa ke tare manyan hanyoyi a birnin don yin abubuwan da ke hana mutane gudanar da harkokinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama matasan bayan sun fara shirin daukar wani bidiyon barkwanci don su samu mabiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
