Yadda Rikicin Kabilanci Ya Jawo Asarar Rayukan Mutane a Taraba

Yadda Rikicin Kabilanci Ya Jawo Asarar Rayukan Mutane a Taraba

  • Rayukan mutane sun salwanta bayan an samu barkewar rikicin kabilanci a jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Rikicin wanda ya ɓarke tsakanin ƙabilun Fulani da Bandawa ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama a ƙaramar hukumar Karim Lamido
  • Dakarun sojoji sun yi ƙoƙarin yin sasanci amma duk da haka rikicin ya ƙara ɓarkewa a tsakanin ƙabilun biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Abin da ya fara a matsayin rikici tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Karim-Lamido ta jihar Taraba ya rikiɗe zuwa mummunan rikicin ƙabilanci.

Aƙalla mutane 40 suka rasa rayukansu, kuma ɗaruruwan mutane suka rasa matsugunansu cikin makonni biyu da suka gabata.

Rikicin kabilanci ya barke a Taraba
Rikicin kabilanci ya jawo asarar rayuka a Taraba Hoto: @AgbuKefas
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ƙabilanci ya auku a Taraba

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin wanda ya fara a ranar 9 ga watan Mayu, ya samo asali ne daga husuma tsakanin wani matashi dan ƙabilar Bandawa mai suna Buhari Malamby da wasu Fulani makiyaya biyu, inda aka ce shanunsu sun kutsa cikin gonarsa.

A sakamakon haka, wasu matasa da dama suka kai hari kan makiyayan da adduna.

Shaidu sun ce Malamby ya rasa ransa yayin arangamar, wanda hakan ya sa matasan Bandawa suka yanka dabbobin Fulani da suka samu a jeji a matsayin ramuwar gayya.

Daga nan sai matasan Fulani ɗauke da makamai suka mamaye ƙauyen Badawa, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wani matashi daga unguwar Munga Dasso.

Jami'an tsaro sun yi sasanci

Jami’an tsaro sun ɗauki mataki cikin gaggawa. A ranar 12 ga watan Mayu, kwamandan runduna ta 6, sashe na 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS), ya kai ziyara kai tsaye don tantance halin da ake ciki a yankin.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya: An kashe rayuka, an kona gidaje a harin ramuwar gayya a Taraba

Sun ziyarci al’ummar Bandawa, sun yi ta’aziyya ga mazauna garin, sannan suka umurci kwamandan rundunarsa da ya aika da sojoji cikin gaggawa zuwa Bandawa da Bunkaci don dawo da zaman lafiya da daƙile zubar da jini.

An kuma tura ƙarin jami’an ƴan sanda, ciki har da na ƴan sandan kwantar da tarzoma, zuwa Munga Dasso.

A kokarin dakile tashin hankali, runduna ta 6 ta shirya taron zaman lafiya a ranakun 15 da 16 ga watan Mayu da manyan masu ruwa da tsaki daga ƙauyukan Bandawa, Munga Dasso, Munga Lelau da Fulani da ke zaune a yankin.

Kwamandan rundunar ya yi gargaɗi mai tsauri ga shugabannin al’umma da su rike matasansu da kuma rage zafin rikicin.

An kammala taron da alƙawarin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a garin Karim-Lamido.

Rikicin ya ƙara ɓarkewa

A ranar 23 ga watan Mayu, aka karya yarjejeniyar bayan wani matashi daga Munga Dasso, aka ce matasan Fulani sun kashe shi a kan hanyarsa ta zuwa gona kusa da wani sansanin Fulani da ke Munga Lelau.

Wannan kisa ya tayar da hankula, inda matasan Munga Lelau suka kai hari sansanin Fulani, suka kashe mutane huɗu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun budewa matafiya wuta a kan hanya, an samu asarar rai

A yayin mayar da martani, wasu gungun matasan Fulani ɗauke da manyan makamai da ke kan babura kusan 50, kowanne ɗauke da mutane uku, suka ƙaddamar da mummunan hari a Munga Lelau.

Sojojin da ke Bunkaci da Bandawa sun mayar da martani cikin gaggawa, suka yi musayar wuta da maharan har suka tilasta musu janyewa cikin ruɗani.

Jihar Taraba
An yi rikicin kabilanci a jihar Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

A yayin mayar da martanin, sojojin sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigan da suka kai harin tare da ƙwato makamai. Sai dai kafin isowarsu, maharan sun riga sun kashe mutane da dama a yankin.

Daga bisani, mahukunta sun saka dokar hana fita daga yamma zuwa Asuba a Bandawa, Munga Dasso, Munga Lelau da wasu ƙauyukan da ke kusa.

An kara yawan sintirin jami’an tsaro domin hana sake aukuwar rikici, kuma ana ci gaba da kokarin gano da kuma cafke wadanda ake zargi da daukar nauyin tashin hankalin.

Rikicin manoma da makiyaya ya ɓarke a Taraba

A wani labarin kuma, kun ji cewa rayuka sun salwanta bayan ɓarkewar wani rikicin Manoma da Makiyaya a jihar Taraba.

Rikicin wanda ya ɓarke a ƙaramar hukumar Karim Lamido ya jawo asarar rayukan aƙalla mutane 16.

Dukkanin ɓangarorin guda biyu sun kai hare-haren ramuwar gayya bayan ɓarkewar rikicin da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng