Rigimar Sarauta Ta Yi Tsami tsakanin Ƴan Uwan Juna, an Kama Mai Ikirarin Kujerar Sarki

Rigimar Sarauta Ta Yi Tsami tsakanin Ƴan Uwan Juna, an Kama Mai Ikirarin Kujerar Sarki

  • Rundunar 'yan sandan Imo ta kama wani basarake mai ikirarin gadon sarauta, Chris Obasi, a gidansa da ke Ajah a Lagos
  • 'Yar uwarsa ta ce rikicin sarauta tsakaninsa da dan uwansa ke haddasa wannan matsala, inda ake kokarin hana gwamnatin jihar amincewa da Obasi
  • Lauyansa, Farfesa Francis Dike, ya ce an zarge shi da daukar nauyin ta'addanci, amma ba za a iya ganinsa ba sai ranar Litinin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Owerri, Imo - Jami’an tsaro sashen 'Tiger Base' na rundunar ‘yan sandan jihar Imo sun kama wani basarake a Lagos.

Rahotanni suka ce an kama basaraken ne da ke ikirarin sarauta a Eziama Ikeduru, Chris Obasi.

An kama mai ikirarin sarauta
Yan sanda sun kama mai ikirarin kujerar sarauta a Lagos. Hoto: Legit.
Source: Original

Dalilin kama basarake a Imo saboda sarauta

’Yar uwarsa, Adaeze Francis, ta tabbatar wa da wakilin Punch cewa an kama Obasi ne da misalin karfe 8 na dare a gidansa da ke Ajah a Lagos.

Kara karanta wannan

Yadda mata suka karbi haramta bikin 'kauyawa day' a Jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce kama shi na da nasaba da rikicin sarauta tsakaninsa da dan uwansa, wanda ke kokarin hana gwamnati amincewa da Obasi a matsayin Sarki.

Ta ce:

“Dukkan lamarin ya shafi rikicin sarauta, dan uwana ne magajin gado na sarautar, domin mahaifinmu marigayi ya rike sarautar kafin rasuwarsa."

Ta ce an nada dan uwanta a matsayin Sarki bayan cikar shekara guda da rasuwar mahaifinsu, amma dan uwansu yana kokarin karbe sarautar da karfi.

Matar ta bayyana cewa an gurfanar da Obasi a gaban kotun majistare saboda rikicin, amma alkalin ya rasu, aka dage shari’ar zuwa 27 ga Mayu, 2025.

Wani dan uwa da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da batun, ya ce dan uwansu ya samu takardar sarauta daga gwamnati ta hanyar siyasa.

“Marigayin ya rasu shekaru hudu da suka gabata, bayan an yi bikin tunawa, sai aka nada Obasi sarki. Amma dan uwansa ya karbe sarautar."

Kara karanta wannan

Ministan Buhari, Amaechi za su jagoranci kwamitocin hadakar yakar jam'iyyar APC

- Cewar majiyar

An cafke wani mai ikirarin kujerar sarauta
Rigimar sarauta tsakanin yan uwa ta kara tsami a Imo. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rigimar sarauta: Lauyan basaraken ya yi magana

Lauyan Obasi, Farfesa Francis Dike (SAN), ya ce rundunar ‘yan sanda ta shaida masa cewa an zargi Obasi da daukar nauyin ta’addanci.

Ya ce:

“’Yan sanda sun ce an rubuta takardar koke a kan Obasi, amma ban gani ba tukuna, sun ce ana zargin sa da daukar nauyin ta’addanci."

Ya ce an shaida masa cewa gwamnati na da hannu a lamarin, kuma ba za a iya ganin Obasi ko neman beli ba har sai ranar Litinin.

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Imo, Henry Okoye, bai yi nasara ba yayin da ba a amsa kira ba.

Rigimar sarauta ta rikice a Enugu

Kun ji cewa rikicin naɗin sarauta a kauyen Isiagu da ke ƙaramar hukumar Nkanu ta Gabas a Enugu ya ƙara zafi duk da an kai ƙara gaban kotu.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suke sa aure tsakanin jaruman Kannywood ke yawan jawo cece kuce

Rahoto ya nuna cewa mazauna garin sun fusata da ganin wata takarda da ke nuna an naɗa Prince Tony Ike Okoye a matsayin sabon Igwe.

A cewarsu, ba zai yiwu a naɗa Okoye ba tare da bin al'ada da ƙa'idojin zaɓe ba, sun roki gwamnatin Enugu ta bari su yi abin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.