Ministan Buhari, Amaechi za Su Jagoranci Kwamitocin Hadakar Yakar Jam'iyyar APC
- Hadakar adawa ta fara nazarin hanyar da za ta fi dacewa wajen fatattakar gwamnatin APC a babban zaben 2027 mai karatowa
- Kungiyar League of Northern Democrats, wacce ta bayyana aniyarta ta tafiya da hadakar, ta ce ana nazarin kafa sabuwar jam’iyya
- Idan ba a cimma wannan muradi ba, akwai wani kwamitin da ke nazarin jam’iyyar da za a iya amfani da ita wajen arangama da APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hadakar ‘yan adawa ta bukaci tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi, da takwaransa na Cross Riba, Liyel Imoke, da su jagoranci nazari a kan matakin da za a dauka kafin 2027.
An dora wa tsofaffin gwamnonin biyu alhakin duba yiwuwar a kafa sabuwar jam’iyya ko kuma su hade da wata jam’iyya domin yakar APC a babban zabe mai zuwa.

Source: Facebook
Punch News ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata sanarwar bayan taron kungiyar League of Northern Democrats ta fitar, wacce shugabanta, Dr Umar Ardo, ya karanta ranar Alhamis a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, da wasu fitattun 'yan siyasa daga Arewacin Najeriya.
Shirin da hadakar adawa ke yi gabanin 2027
Dr Ardo ya ce Liyel Imoke ne ke jagorantar kwamitin da ke nazarin yiwuwar hadewa da wata jam’iyya, yayin da Rotimi Amaechi ke jagorantar kwamitin da ke duba yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya.
Shugaban kungiyar LND ya ce za a yanke hukunci na karshe kan ko hadakar za ta kafa sabuwar jam’iyya ko ta hade da wata da ke akwai a ranar 30 ga watan Mayu.

Source: Facebook
Ya ce:
“Mun yanke shawarar goyon bayan hadakar adawa domin siyasar sauyi a zaben 2027 da kuma bayar da gudunmuwa a tattaunawar kan ko a kafa sabuwar jam’iyya ko a hade da wata jam’iyya da ke akwai."
"Hadakar ta kafa kwamitoci biyu, domin su nazarci yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya da kuma yiwuwar hade da wata jam’iyya da ke akwai. Dukkanin kwamitocin sun mika rahotonsu.”
Hadakar adawa: Ana duba yiwuwar shiga ADC
Dr Ardo ya bayyana cewa har yanzu suna duba jam’iyyu kamar su ADC da SDP a matsayin jam'iyyar da za a yi amfani da su domin cimma muradin hadakar.
Ya ce:
“Mun kuma yanke shawarar tuntubar gwamnonin Arewa 19 kan matsanancin halin da yankin ke ciki – talauci, barace-barace, rashin tsaro da rashin aikin yi da suka addabi Arewacin Najeriya. Mafi yawanmu mun yarda cewa babban matsalar ita ce sakacin gwamnoninmu 19 na Arewa.”
Ana son Obi ya watsar da hadakar adawa
A baya, mun wallafa cewa Ministan ayyuka na tarayya, Dave Umahi, ya bukaci tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, da ya marawa Bola Tinubu baya.
Umahi ya kara da cewa ya kamata Obi ya hada kai da sauran shugabannin yankin Kudu maso Gabas domin karfafa tafiyarsu, musamman gabanin zaben 2027.
Ministan ya ce duk da bambancin jam’iyyu, mafi yawan shugabannin Kudu maso Gabas na goyon bayan gwamnatin Tinubu saboda irin ayyukan raya kasa da ake gani a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

