'Yan Sandan Kano Sun Gwabza da Yan Ta'adda, An Ceto Baiwar Allah bayan an Sha Gumurzu
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta samu nasarar kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita daga jihar zuwa Jigawa
- Rundunar ta ce ta cafke wasu daga cikin masu garkuwar yayin wani samame da suka kai cikin dajin a kokarinsu na koro miyagu
- Nasarar ta yiwa jama'a dadi, inda da dama suka yabawa rundunar ‘yan sandan Kano bisa jajircewarta wajen yaki da aikata laifi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kubutar da wata mata da aka yi garkuwa da ita, tare da cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta kara da cewa an sace matar ne daga garin Minjibir da ke Kano, inda aka kaita cikin dajin Garki da ke makwabciyar jihar Jigawa.

Kara karanta wannan
'Yana cikin hatsari': Iyalan Sarki da aka sace sun fara neman taimakon kuɗin fansa

Source: Facebook
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan sandan Kano sun fafata da 'yan bindiga
Jaridar Leadership ta wallafa cewa jami’an ‘yan sanda sun kutsa cikin dajin inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutane.
A yayin fafatawar, an harbe wasu daga cikin masu garkuwar, yayin da aka cafke ragowar, sannan kuma, an samu nasarar kubutar da matar ba tare da wata illa ba.
SP Kiyawa ya ce:
“Sun yi garkuwa da wata mata, sun dauke ta daga garin Minjibir zuwa jihar Jigawa. An harbe wasu daga cikinsu, an kamo wasu. Ita kuma cikin ikon Allah an ceto ta. An samu makamai a hannunsu. Muna godiya ga Allah (SWT).”
Jama’a sun yaba da jajircewar ‘yan sandan Kano
Bayan bayyana wannan nasara, jama’a da dama sun nuna jin dadinsu da yabawa da jajircewar da rundunar ‘yan sandan Kano ke nunawa, musamman a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
Aliyu Sulaiman Yusuf ya ce:
“Wannan nasarar da hukumar ‘yan sanda jihar Kano ke samu yana da alaka da yin aiki tukuru, adalci, gaskiya da rikon amana.”
Habib Jibrin Yanchibi ya ce:
“Alhamdulillah, Allah ya ƙara tona asirinsu.”
Salisu Yusuf Ajiya ya wallafa:
“Abin har ya kai Kano? Allah ya kyauta.”
Anas Abdullahi ya ce:
“Masha Allah, muna rokon Allah Ubangiji ya cigaba da bawa jami’an tsaronmu sa’a akan duk masu aikata laifi. Amin.”
Kaab Tijjani ya yi addu’a:
“Ya Allah ka kawo mana shiryarwa cikin al’ummarmu. Amma fa wallahi da laifi shuwaga banni cikin lalacewar wannan al’umma.”
Hauwa Musa Abdullahi ta ce:
“A tafawa ‘yan sandan jihar Kano. Kamar su kadai ke aiki a fadin Nigeria.”
Rundunar ‘yan sanda ta Kano na ci gaba da kira ga jama’a da su rika bayar da hadin kai da bayanai domin kara tabbatar da tsaro a fadin jihar.
'Yan sanda sun yi kame a Kano
A baya, mun wallafa cewa wasu bata-garin matasa sun kashe malamin addini kuma kwararre a fannin fasaha, Alaramma Jabir Lawan Abdullahi, a birnin Kano.
Rahotanni sun nuna cewa an sokawa malamin wuka sau da dama yayin wata haramtacciyar kilisa da aka gudanar a Unguwar gidan Sarki a ranar Asabar din da ta gabata.
A farko, rahotanni sun nuna cewa an kai wa malamin hari ne da nufin sace masa waya a lokacin da yake cikin adaidaita sahu a cunkoson ababen hawa, kamar yadda aka saba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

