Sauki Na Tafe: Dangote zai Cigaba da Rage Farashin Man Fetur a Najeriya
- Matatar Dangote da ke Legas ta ce za ta ci gaba da rage farashin fetur duk da hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya
- Kamfanin ya ce matakin yana nuna ƙudurinsa na tallafa wa tattalin arzikin Najeriya da saukaka wa 'yan ƙasa a kan halin da suke ciki
- Dangote ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa shirin sayar masa da danyen mai da Naira da ya bai wa kamfanin damar sauke farashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matatar Dangote ta tabbatar da aniyar na ci gaba da rage farashin man fetur duk da sauye-sauyen da ake samu a farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Matatar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in hulɗa da jama’a na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina ya fitar a ranar Litinin.

Source: Getty Images
Rahoton Arise News ya nuna cewa Anthony Chiejina ya mika godiya ga Bola Tinubu a madadin Aliko Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kamfanin, wannan mataki wani ɓangare ne na goyon bayan da yake bai wa tattalin arzikin Najeriya da kuma rage wa ‘yan ƙasa nauyin hauhawar farashin man fetur.
Dangote na tallafa wa tattalin Najeriya
Sanarwar ta bayyana cewa matakin rage farashin fetur yana da alaƙa da manufar gwamnatin tarayya na fifita kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.
Businees Day ta wallafa cewa Dangote ya ce:
“Ta hanyar tace danyen mai a cikin gida a matatarmu... Muna alfahari da irin gudunmawar da muke bayarwa wajen inganta makamashi, rage kashe kudi a ketare, da kuma daidaita tattalin arzikin ƙasa.”
Kamfanin ya ce za a ci gaba da samun saukin farashin ne bisa goyon bayan da ya samu daga gwamnatin Bola Tinubu, musamman ta hanyar tsarin sayar masa da danyen mai da Naira.

Source: Twitter
Dangote ya ce farashin mai zai kara sauka
Dangote ya jaddada cewa kamfanin na da niyyar ci gaba da samar da mai da araha, mai inganci da kuma mai dorewa, ba tare da rage ingancinsa ba.
Matatar Dangote ta ce:
“Mun jajirce wajen tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun amfana da damar da ke tattare da tace mai a cikin gida,”
Dangote ya kara da cewa kamfanin zai ci gaba da sanya bukatun kasa da jin dadin jama’a a gaba, yana mai cewa:
“Za mu ci gaba da fifita araha, inganci, da muradun kasa a kowane fanni na ayyukan mu.”
Kamfanin ya tabbatar wa da masu amfani da mai, abokan hulɗa da gwamnati cewa zai ci gaba da ba da cikakken gudunmawa wajen tabbatar da jin daɗin al’umma da dorewar ci gaban ƙasa.
Su Dangote sun mallaki kamfani a Kenya
A wani rahoton, kun ji cewa Aliko Dangote da wani abokinsa sun mallaki wani katafaren kamfanin yawo bude ido a kasar Kenya.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin shi ne mafi girma kuma mafi dadewa a cikin kamfanonin bude ido a kasar gabashin Afrikar.
Ana sa ran cewa ba wanda zai rasa aikinsa a kamfanin sakamakon sayen shi da Alhaji Aliko Dangote da Dave Rubenstein suka yi.
Asali: Legit.ng


