Vatican: Bidiyon Yadda Aka Hana Peter Obi Shiga Fadar Fafaroma, sai da Tinubu Ya Roƙa

Vatican: Bidiyon Yadda Aka Hana Peter Obi Shiga Fadar Fafaroma, sai da Tinubu Ya Roƙa

  • Wasu majiyoyi sun ce an hana Peter Obi shiga fadar Vatican, inda aka rantsar da sabon Fafaroma Leo XIV, bayan mutuwar Francis
  • An ce jami’an tsaro sun dakatar da Obi a kofar fadar duk da roƙon Rabaran Francis Arinze, har sai da Bola Tinubu ya sa baki aka bar shi
  • Femi Fani-Kayode ya ce ba a bar 'dan siyasar ya gana da Fafaroma ba, sai dai ya gaishe da Shugaban kasa Bola Tinubu da ke wurin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Rome, Italy - Wasu majiyoyi sun ce dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya sha kunya a fadar Vatican da ke birnin Rome a Italiya.

An ce jami'an tsaro da ke gadin mashigar fadar sun hana Obi shiga ciki bayan ya je bikin rantsar da Fafaroma.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya haɗu da Peter Obi a bikin naɗin Fafaroma, an ji abin da suka tattauna

Tinubu ya taimakawa Obi a fadar Vatican
Yadda Tinubu ya sa baki aka bar Obi ya shiga fadar Vatican. Hoto: @aonanuga1956.
Source: Twitter

Tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya wallafa bidiyon a shafin X a daren jiya Litinin 19 ga watan Mayun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan baki da suka halarci rantsar da Fafaroma

An rantsar da Fafaroma Leo XIV ne a ranar Litinin 19 ga watan Mayun 2025 bayan mutuwar magabacinsa Francis.

Sabon Fafaroman musamman ya gayyaci shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu domin halartar bikin a birnin Rome.

Bikin ya samu halartar manyan baki daga ko ina a fadin duniya da kuma mabiya darikar katolika.

Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da kuma tsohon gwamnan Ekiti, Dr. Kayode Fayemi suna daga cikin mahalarta taron.

Yadda Tinubu ya taimaki Obi a fadar Vatican
Tinubu ya sa baki aka bar Obi ya shiga fadar Vatican. Hoto: @peterobi.
Source: UGC

Yadda aka hana Peter Obi shiga fadar Vatican

A cikin bidiyon, an gano yadda aka tare Peter Obi duk da rokon da babban Fasto a fadar, Rabaran Francis Arinze ya yi.

Fani-Kayode ya ce sai da Bola Tinubu ya sanya baki kafin aka bar Obi ya shige fadar jagoran kiristocin duniyan a cikin sauki.

Kara karanta wannan

Tinubu da Musulman shugabanni da suka halarci rantsar da Fafaroma Leo XIV

Ya ce duk da shiga cikin fadar, ba a bar Obi ya je wurin Fafaroma ba sai dai ya je ya gaishe da Tinubu.

Fani-Kayode ya yi rubutu kamar haka:

Duk da ƙoƙarin Rabaran Arinze, alamu sun nuna cewa ba a bar Peter Obi ya gana da Fafaroma ba.
"An hana shi shiga cikin fadar Vatican har sai da Bola Tinubu ya sa baki, sannan aka bar shi ya shiga ya gaishe shi.
"Amma ko da hakan, ba a bar shi kusa da Fafaroma ba, sai dai ya je ya gaishe da Shugaban kasarmu.
"Obidients, ku lura, ku je inda ake karɓarku da hannu biyu, ba inda ake ɗaukarku kawai saboda ladabi ba."

Abin da Tinubu ya tattauna da Obi, Fayemi

Mun ba ku labarin cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya haɗu da tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi da Dr. Kayode Fayemi a wurin bikin naɗa sabon Fafaroma.

An na sabon Fafaroma Leo XIV ne bayan mutuwar tsohon wanda ya rasu a karshen watan Afrilun 2025 da ta gabata.

Majiyoyi sun nuna cewa Kayode Fayemi da Mista Obi sun je har wurin da Bola Tinubu ke zaune a taron inda suka gaisa da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.