Mukaddashin Shugaban Karamar Hukuma Ya Rasu a Bauchi ana Saura 'Yan Kwanaki Zabe

Mukaddashin Shugaban Karamar Hukuma Ya Rasu a Bauchi ana Saura 'Yan Kwanaki Zabe

  • Allah ya yi Muƙaddadin shugaban ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi, Alhaji Wali Adamu ya yi bankwana da duniya
  • Marigayin ya rasu ne bayan ya yi fama da ƴar gajeriyar jinyar rashin lafiya a ranar Lahadi, 11 ga watan Mayun 2025
  • Rasuwar Alhaji Adamu Wali na zuwa ne yayin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ke shirin gudanar da zaɓen cike gurbi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Muƙaddashin shugaban ƙaramar hukumar Shira da ke jihar Bauchi, Alhaji Wali Adamu, ya yi bankwana da duniya.

Wali Adamu ya rasu ne a ranar Lahadi a cibiyar kiwon lafiya ta tarayya da ke Azare, ƙaramar hukumar Katagum, jihar Bauchi, bayan gajerar rashin lafiya.

Alhaji Wali Adamu ya rasu
Shugaban riko na karamar hukuma Shira, Alhaji Wali Adamu ya rasu Hoto: Mukhtar Gidado
Source: Facebook

An yi rashin shugaba a jihar Bauchi

Sanarwar rasuwarsa ta fito ne a ranar Lahadi ta bakin mai ba gwamnan jihar Bauchi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya koka kan gagarumar matsalar da ta tunkaro matasan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Wali Adamu ya zama muƙaddashin shugaban karamar hukumar ne bayan da a ranar 3 ga Maris, 2025, aka tsige tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Abdullahi Ibrahim Beli, da mataimakinsa, Hon. Usman Adamu.

An tsige shugaban da mataimakinsa ne bisa zargin rashin ɗa’a, almundahana da kuɗaɗe, sakacin aiki, da kuma amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba.

Kafin naɗinsa, Adamu Wali ya kasance kansila mai wakiltar gundumar Tumfafi, kuma shine shugaban majalisar ƙaramar hukumar a wancan lokaci.

Gwamnan Bauchi, Bala ya yi ta'aziyya

A cikin saƙonsa na ta’aziyya ga iyalan marigayin, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana marigayi Alhaji Wali Adamu a matsayin shugaban jama’a mai kishin ƙasa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa ba za a manta da gudunmawarsa wajen ci gaban karamar hukumar Shira da jihar Bauchi ba.

“Gwamna Bala Mohammed, a madadin gwamnatin jihar Bauchi da ɗaukacin al’ummar jihar, na miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Wali Adamu, majalisar sarakunan gargajiya na masarautar Katagum, da dukkan al’ummar jihar bisa wannan babban rashi."

Kara karanta wannan

Abbas Tajudeen: Shugaban majalisar wakilai ya yi babban rashi a rayuwarsa

- Mukhtar Gidado

Gwamnatin jihar Bauchi ta kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da saka iyalan marigayin cikin addu’a a wannan lokacin mai wahala a gare su.

Bala Mohammed ya kuma yi addu’ar Allah Ya ji ƙan marigayin da rahama, ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashi.

Alhaji Wali Adamu
Alhaji Wali Adamu ya rasu Hoto: Mukhtar Gidado
Source: Facebook

Wali Adamu ya rasu ana dab da zaɓe

Rasuwar Adamu Wali ta zo ne kwana 13 kafin ranar zaben cike gurbin shugaban ƙaramar hukumar da za a gudanar a Shira, cewar rahoton jaridar Leadership.

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC), Ahmed Makama, ya bayyana a baya cewa hukumar ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen cike gurbi a ranar 24 ga watan Mayu, 2025.

Hukumar zaɓe ta BASIEC dai ta gudanar da zaɓen shugabanni da mataimakansu a dukkanin ƙananan hukumomi 20 na jihar Bauchi a watan Agusta, 2024.

Tsohon gwamna ya rasu a shekara 89

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Chief Omololu Ogunloyo, ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Bankwana da siyasa: Shugaban malamai a Izala, Sheikh Dalha ya fita daga APC

Marigayin ya yi bankwana da duniya ne yana saura ƴan kwanaki kaɗan ya cika shekara 90 da haihuwa.

Chief Omololu Ogunloyo ya rasu ne a ranar Asabar, 5 ga watan Afirilun 2025, inda ya bar ƴaƴa da jikoki da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng