'Yan Bindiga Sun Tare Motoci a Babban Titi a Najeriya, Sun Ƙona Mutane da Ransu

'Yan Bindiga Sun Tare Motoci a Babban Titi a Najeriya, Sun Ƙona Mutane da Ransu

  • Ƴan bindiga sun tare motoci a kan wani babban titi a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, sun bankawa motoci wuta
  • An ruwaito cewa maharan sun hallaka mutane da dama da suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, sun ƙona wasu a harin na ranar Alhamis
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ɗora alhakin kai harin kan ƙungiyar ƴan aware watau IPOB

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Mutane da dama sun rasa rayukansu da safiyar ranar Alhamis lokacin da wasu 'yan bindiga suka tare hanya a ƙaramar hukumar Okigwe da ke jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya.

Ƴan ta'addan, waɗanda ake zargin ƴan haramtacciyar kungiyar aware ne watau IPOB sun kashe mutane tare da ƙona motoci da dama a harin na rashin imani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka basarake a wani harin ta'addanci a Benue

Taswirar Imo.
Yan bindiga sun kashe mutane da yawa a harin da suka kai kan titin Okigwe-Owerri a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƴan bindiga sun ƙona matafiya a motoci

Rahotan Premium Times ya nuna cewa maharan sun tsayar da motoci tare da banka masu wuta a kan babban titin Okigwe-Owerri.

Lamarin ya faru ne a tsakanin ƙauyen Umuna da ke a ƙaramar hukumar Onuimo da kauyen Amuro a ƙaramar hukumar Okigwe a jihar Imo.

Shaidun gani da ido sun ce ƴan bindigar sun kashe mutane da yawa, musamman lokacin da jami’an tsaro suka gwabza da maharan.

Ƴan sanda da sojoji sun gwabza da maharan

Augustine Mbanusi, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa aƙalla motoci 20 galibinsu manyan tifa da tireloli sun ƙone a harin.

"’Yan sanda da sojoji sun yi ƙoƙarin faɗa masu, amma kusan mutane 30 ne aka kashe,” in ji Mbanusi cikin harshen Igbo.

Wani bidiyo da ke yawo ya nuna yadda wuta ke ci gaba da ƙone motocin, inda ake jin muryoyin mutane suna nuna alhininsu, suna cewa wasu sun makale a motoci har suka kone kurmus.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka babban soja a wani hari a Borno

“Mutane har yanzu suna makale a ciki. Da muna da ruwa, da mun zuba a kansu,” wata murya ta bayyana a cikin harshen Igbo.
Yan sanda.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da harin ƴan bindigar Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

Rundunar ƴan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da harin da kuma mutuwar mutane, sai dai bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba.

"Maharan sun zo ne a rukunoni uku, suka tare hanyar, suna harbe-harbe ba kakkautawa, suka firgita mutane, sannan suka ƙone motoci da babura,” in ji shi.

Okoye ya ƙara da cewa rundunar ƴan sanda na zargin maharan ƴan haramtacciyar ƙungiyar IPOB ne, kamar yadda The Cable ta tattaro.

Ƴan bindiga sun sace limamin katolika a Imo

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da limamin cocin katolika, Rabaran John Ubaechu, a Ejemekwuru, karamar hukumar Oguta da ke jihar Imo.

A ruwaito cewa maharan sun sace Ubaechu, fasto a Cocin Holy Family Catholic da ke Izombe, a kan hanyarsa ta zuwa taron shekara-shekara na fastoci.

Rundunar ’yan sandan jihar Imo ta tabbatar da sace faston, inda ta bayyana cewa an sace shi ne a kan titin Ejemekwuru da ke Oguta a jihar Imo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262