Abin Boye Ya Fito: Rundunar Tsaro Ta Faɗi Wadanda Ke Kai Hare Hare a Jihohin Arewa

Abin Boye Ya Fito: Rundunar Tsaro Ta Faɗi Wadanda Ke Kai Hare Hare a Jihohin Arewa

  • Rundunar tsaro ta ce makiyayan waje ne ke kai hari a jihohin Benue da Plateau, sun Najeriya ta iyakoki masu rauni
  • Sojoji sun kama fitattun masu garkuwa da mutane da dillalan makamai, ciki har da wani 'dan ta'adda mai suna Nkwachi Eze
  • An ji cewa an ceto mutane 173 da aka sace, an kama masu laifi 430, an kuma dakile satar man da ya kai sama da N1.9bn

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta yi magana game da ayyukan ta'addanci a Najeriya musamman a Arewacin ƙasar.

Rundunar tsaron ta fadi wadanda ake zargi da kai hare-hare da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.

Rundunar tsaro ta yi magana kan hare-hare
Rundunar tsaro ta fadi masu kai hare-hare. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Twitter

Su wanene ke kawo hare-hare Najeriya?

Daraktan hulda da jama'a, Markus Kangye shi ya fadi haka a taron manema labarai a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan kyaftin ɗin soja, ƴan bindiga sun hallaka sufetan ɗan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kangye ya danganta yawan hare-haren da ake kaiwa kan al’ummomi a Benue, Plateau da sauran wurare da makiyayan waje da suka shigo Najeriya.

Ya ce:

"Misali, idan na yi Hausa kuma dan uwana daga Kudu maso Gabas ya yi Hausa, zaka san wannan ba Hausar asali ba ce.
“Idan wani daga Sokoto ya yi Hausa, sannan wani daga Katsina ya yi, za ka fahimci bambanci tsakanin sautukan su da yadda suke fada.
“Hausa da muke yi a Najeriya ba daya ba ce da wadda ake yi a Mali, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Ghana.”

Yadda ake gane inda 'yan ta'adda suka fito

Kangye ya kara da cewa ba kawai yaren su ba, har ma da yadda gashinsu yake yana nuna ba ‘yan Najeriya ba ne.

Ya ce idan suka kama sukan gane ba 'yan Najeriya ba ne daga yadda suke magana da kuma gashinsu.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

An fara kera makaman yaki a Najeriya, sufeton 'yan sanda ya ziyarci masana'antar

“Don haka idan muka kama wadannan makiyaya ko ‘yan ta’adda, daga maganarsu da gashinsu za ka gane ba daga Najeriya su ke ba.
“Ina ganin kabilar da kadai a Najeriya da gashinsu ya dan yi kama da na Shuwa daga yankin Sahel, su ne Shuwa Arab."
Rundunar tsaro ta fayyace masu kawo hare-hare
Rundunar Tsaro ta tona asirin masu kawo hare-hare. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Rashin tsaro: Rundunar sojoji ta nemi hadin kai

Kangye ya bukaci hadin gwiwar hukumomin tsaro domin kula da iyakokin Najeriya tare da tabbatar da cewa an san duk wanda ya shigo.

Ya bayyana kama wani shahararren mai safarar makamai da garkuwa da mutane, Buhari Umar, wanda ke addabar mutane a jihohin Gombe da Bauchi.

Sojoji sun kuma kama wani rukuni na masu garkuwa da mutane guda biyar a karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa.

Badaru ya magantu kan ingancin makaman sojoji

Kun ji cewa Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi magana kan kalaman da wasu ƴan majalisa suka yi na cewa makaman ƴan ta'adda sun fi na sojoji.

Badaru ya bayyana cewa ko kaɗan batun ba haka yake ba domin akwai rata mai nisa wajen riƙe makamai tsakanin sojoji da ƴan ta'adda.

Ministan ya bayyana cewa suna ƙara azama wajen samar da kayan aiki waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.