Ministan Tsaro Ya Raba Gardama kan Batun 'Yan Ta'adda Sun Fi Sojoji Makamai

Ministan Tsaro Ya Raba Gardama kan Batun 'Yan Ta'adda Sun Fi Sojoji Makamai

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi martani kan kalaman da wasu ƴan majalisa suka yi na cewa makaman ƴan ta'adda sun fi na sojoji
  • Mohammed Badaru ya bayyana cewa ko kaɗan batun ba haka yake ba domin akwai rata mai nisa wajen riƙe makamai tsakanin sojoji da ƴan ta'adda
  • Babban Ministan ya bayyana cewa suna ƙara azama wajen samar da kayan aiki waɗanda za su taimaka wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'adda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi magana kan batun cewa ƴan ta'adda sun fi sojojin Najeriya riƙe makamai.

Mohammed Badaru ya musanta iƙirarin da ƴan majalisar wakilai suka yi na cewa makaman ƴan ta’adda sun fi na sojojin Najeriya.

Mohammed Badaru
Badaru ya ce makaman sojoji sun fi na 'yan ta'adda Hoto: Mohammed Badaru Abubakar
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, Badaru ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun fi ƴan ta’adda kayan yaƙi da kuma fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda a Katsina, an samu asarar rayuka

A ranar Talata, majalisar wakilai ta bayyana damuwa kan harin da aka kai wa sansanin sojoji, inda ta bayyana hakan a matsayin alamar cewa ƴan Boko Haram sun fi sojoji kayan yaƙi.

Ministan tsaro ya yi magana kan yaƙar ƴan ta'adda

Ministan ya ce matsalar da ake fuskanta ba rashin makamai ba ne, sai dai dabarun da ƴan ta’addan ke amfani da su, wanda galibi ana samun su ne ta hanyar bayanan sirri daga mazauna yankunan da abin ya shafa.

"Jiya majalisar wakilai da majalisar dattawa sun ce ƴan ta’adda sun fi mu makamai."
"Wannan ba gaskiya ba ne. Muna da makamai na zamani fiye da nasu. Muna da jiragen yaƙi marasa matuƙa fiye da nasu."
“Abin da ke faruwa shi ne, wannan ba yaƙi ba ne na gaba da gaba. Yaƙin sunƙuru ne. Suna bibiyar motsinmu, suna da masu ba su bayani a cikin al’umma."

Kara karanta wannan

Gwamna ya samo mafita ga sojoji kan matsalar rashin tsaro

“Suna taimakawa waɗanda muke ƙoƙarin karewa, suna ba su bayanai. Sannan suna kai mana farmaki ba tare da mun yi tsammani ba."

- Mohammed Badaru Abubakar

Mohammed Badaru
Badaru ya ce 'yan ta'adda ba su kai sojojin Najeriya makamai ba Hoto: Mohammed Badaru Abubakar
Source: Facebook

Shin ƴan ta'adda na amfani da jirage marasa matuƙa?

Badaru ya kuma taɓo batun amfani da jirage marasa matuƙa da ƴan ta’adda ke yi, inda ya bayyana cewa har yanzu suna amfani da ƴan ƙananan jirage ne waɗanda suke sanya bam a cikinsu, rahoton Vanguard ya tabbatar.

“Ba sa amfani da jirage marasa matuƙa na soja. Muna ƙara ƙoƙari wajen tattara bayanan leƙen asiri, a gida da kuma waje, don daƙile hanyoyin samun makamai."

- Mohammed Badaru Abubakar

Ya kamata sojoji su tashi tsaye

Abubakar Mikail ya gayawa Legit Hausa cewa ya kamata a ƙarawa sojojin Najeriya kayan aiki domin magance matsalar rashin tsaro.

"Ƴan ta'adda suna amfani da manyan makamai, wani lokacin ma su kan fi na sojojin Najeriya. Hakan ya nuna buƙatar a ƙara musu kayan aiki."
"Idan ba kayan aiki babu yadda za a yi su samu nasarar kan ƴan ta'adda da suka daɗe suna addabar mutane."

Kara karanta wannan

Ganduje ya tabo batun maida Najeriya karkashin jam'iyya 1, ya fadi shirin APC

- Abubakar Mikail

Babban hafsan sojojin ƙasa ya koma Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya koma fagen daga a jihar Borno.

Shugaban sojojin ya koma jihar ne tare da manyan kwamandojinsa domin lura da yadda ake fafatawa da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP.

Komawar tasa za kuma ta taimaka wajen fito da sababbin dabaru domin ganin an kawo ƙarshen ragowar ƴan ta'addan da suka rage.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng