Matawalle Ya Bayyana Adadin 'Yan Ta'addan da Aka Kashe a Gwamnatin Tinubu
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu
- Matawalle ya bayyana cewa an kashe ƴan ta'adda masu tarin yawa a ƙarƙashin Bola Tinubu a shekarar 2024
- Ministan ya nuna cewa nasarorin da shugaban ƙasan ya samu, za su iya sanyawa a sake zaɓensa a shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana adadin ƴan ta'addan da aka kashe a gwamnatin Bola Tinubu.
Bello Matawalle ya bayyana cewa aƙalla ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane fiye da 8,000 ne aka kashe a faɗin Najeriya a shekarar 2024 ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Patience Ituke ta fitar a madadin daraktan hulɗa da jama’a na ma’aikatar tsaro a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake nazari kan yadda gwamnatin yanzu ke tafiya, Matawalle ya danganta gagarumar nasarar da aka samu a fannin tsaro da sababbin dabarun aiki da gwamnatin Tinubu ta kawo.
Ƴan ta'adda nawa aka kashe a ƙarƙashin Tinubu?
Ya ƙara da cewa ban da kashe ƴan ta’addan, an cafke fiye da mutane 11,600 da suka aikata laifuka, sannan jami’an tsaro sun ƙwato bindigogi da makamai fiye da 10,000 a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Matawalle ya jaddada cewa nasarorin da gwamnati ke samu wajen yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane, da sauran nasarorin da Shugaba Tinubu ya cimma, za su iya tabbatar masa da wa’adin mulki na biyu a shekarar 2027.
"Bello Matawalle ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sauye-sauyen da ya kawo, yana mai cewa waɗannan matakai za su samar da makoma mai kyau ga Najeriya tare da yiwuwar sake zaɓensa a 2027."
“Minista Matawalle ya bayyana wasu muhimman nasarori da gwamnatin Tinubu ta cimma, musamman a bangaren tsaro."

Kara karanta wannan
Hadakar Atiku ta fara gigita APC, an fallasa abin da Tinubu ke kullawa 'yan adawa
"Ya bayyana nasarar da aka samu wajen kashe fiye da ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane 8,000, kama masu laifi 11,600, da kuma kwato makamai fiye da 10,000 a shekarar 2024."
- Patience Ituke

Source: Facebook
Bello Matawalle ya faɗi nasarorin Tinubu
Ya kuma bayyana wasu nasarorin gwamnatin Tinubu, ciki har da kafa ma’aikatar kiwon dabbobi, wacce ya ce ta riga ta fara rage farashin hatsi da ƙarfafa noman zamani a Arewacin Najeriya.
“Matawalle ya kuma yabawa ƙoƙarin gwamnati a fannin tattalin arziƙi, musamman wajen kafa ma’aikatar kiwon dabbobi, da nufin amfani da damar noma da kiwo da Arewacin ƙasar nan ke da shi, haɓaka tattalin arziki da kuma ƙarfafa miliyoyin ƴan Najeriya."
- Patience Ituke
Sanata Ali Ndume ya yabi Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya nuna jin daɗinsa kan matakin da Bola Tinubu ya ɗauka.
Ndume ya yabawa shugaban ƙasan kan dakatar da shigo da kayayyaki daga waje waɗanda za a iya samarwa a cikin gida.
Sanatan ya bayyana cewa wannan matakin zai taimakawa masana'antun cikin gida tare da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
