Rashin Tsaro: An Kai Ruwa Rana tsakanin Gwamna da Majalisa bayan Dawowa Hutu

Rashin Tsaro: An Kai Ruwa Rana tsakanin Gwamna da Majalisa bayan Dawowa Hutu

  • Majalisar Wakilai ta zargi Gwamna Alia Hyacinth da watsi da dokar hana kiwo a fili, wanda ke haddasa kashe-kashe a jihar Benue
  • Majalisar ta gayyaci gwamnonin Benue da Zamfara su bayyana gabanta kan dalilin da yasa ba za a kwace ayyukan majalisunsu ba
  • An ce Sanatoci za su mayar da hankali kan dokokin haraji da matsalar tsaro da ke addabar Benue, Plateau da Borno bayan dawowar hutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yayin da ta dawo daga dogon hutu yau, Majalisar Wakilai da Gwamnatin Jihar Benue sun saba kan dalilan kashe-kashen da ke faruwa.

Mataimakin mai magana da yawun Majalisar, Philip Agbese ya zargi Gwamna Hyacinth Alia da watsi da dokar hana kiwo a fili wanda ya jawo rikice-rikice.

Majalisa ta kalubalanci gwamna kan rashin tsaro
Rashin tsaro: An kai ruwa rana da gwamna. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Ɗan majalisa ya kalubalanci gwamna Alia

Kara karanta wannan

Bashin Naira tiriliyan 4: Gwamnatin Najeriya ta fara hararo karin kudin wuta

Gwamnan ya mayar da martani yana cewa Agbese bai fahimci yadda dokoki ke aiki a majalisa ba, yana mai cewa ba shi da hujja, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana, Agbese ya ce majalisar ta kuduri aniyar kare rayukan 'yan Najeriya da dukiyoyinsu daga hare-haren ’yan ta’adda.

Ya ce:

“Yayin da muke dawowa gobe (Talata), mun shirya fuskantar matsalar tsaro da gaske. Mun gaji da yin shiru na mintuna domin girmama matattu.
“Za mu sanar da gwamnati matsalolin da ke faruwa ta hanyar daukar matakan gaggawa. Muna so mu ga mataki, ba wai kalamai kawai ba.
“Idan muka fahimci babu sababbin dabaru daga shugabannin tsaro, za mu shawarci Shugaban kasa ya sauke su, ya nada sababin mutane.”

Game da kashe-kashen a Benue, Agbese ya zargi Gwamna Alia da watsi da dokar hana kiwo a fili, yana cewa yana fakewa da yarjejeniyar ECOWAS.

Gwamna ya soki ɗan majalisa kan rashin tsaro
Rashin Tsaro: Gwamna Alia ya caccaki ɗan majalisa. Hoto: Alia Iormem Hyacinth.
Source: Twitter

Gwamna Alia ya dura kan ɗan majalisa

Gwamna Alia ya ce Agbese bai fahimci dimokradiyya ba, ta bakin mai ba shi shawara, Iorpev, ya ce babu sauya ta ba tare da bin tsarin doka ba.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

Ya ce:

“A tsarin soja ne ake cire doka haka kawai. Amma a dimokradiyya dole sai an bi ka’ida kafin sauya doka.”

Iorpev ya kara da cewa Gwamna ya sha bayyana cewa yana goyon bayan cikakken aiwatar da dokar hana kiwo a fili a Benue.

Majalisar Dokokin Jihar Benue za ta yanke hukunci yau kan ko za ta amsa gayyatar Majalisar Wakilai ko a’a, cewar Daily Post.

Shugaban Majalisar Dokoki na Benue, Dajoh Hyacinth, ya ce a ranar Litinin ya samu gayyatar kuma zai gabatar da ita ga majalisa yau.

Gwamnan Benue ya bukaci taimakon Tinubu

Kun ji cewa Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya ce abin da al’ummarsa ke buƙata yanzu shi ne cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya, ba dokar ta-baci ba.

Gwamnan ya ce matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar ba ta fi ƙarfinsa ba, amma yana neman taimako sosai domin ya kori makiyaya masu ɗauke da makamai a fadin jihar.

Alia ya jaddada cewa gwamnatinsa ta rage yawan kananan hukumomin da ake kai hare-hare daga 17 zuwa shida rak bayan hawansa kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.