Kasafin Kudin 2025 a Najeriya Zai Iya Cin Karo da Matsala da Farashin Mai Ya Faɗi
- Farashin danyen mai ya fadi zuwa kasa da $60, abin da ke barazana ga kasafin kudin gwamnatin tarayya da na jihohi a 2025
- Najeriya na fama da faduwar yawan hakar mai zuwa kasa da ganga miliyan 1.5 a rana, adadin da bai kai abin da aka yi tsammani ba
- Kamfanonin man duniya sun bayyana ragin da kuma ribar su, yayin da masana ke gargadi gibin kudin Najeriya zai iya kai N30.79trn
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Farashin danyen mai ya fadi kasa da $60 kan ganga, wanda ya haddasa damuwa game da yadda gwamnatin tarayya da jihohi za su iya daukar nauyin kasafin kudinsu na 2025.
An kiyasta kasafin kudin zuwa N75trn domin inganta kasa ba tare da kara cin bashi ba.

Source: Facebook
Yadda aka tsara kasafin kudin 2025

Kara karanta wannan
Bayan rahotonsa a kan karuwar talaucin Najeriya, Bankin Duniya ya ba Tinubu lakani
Faduwar farashin man ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsin lamba na kara yawan hakar man ta fiye da ganga miliyan 1.5 a rana, cewar The Guardian.
Tun farko an sanya fitar da ganga miliyan 2.06 a matsayin ma’auni a kasafin kudin shekarar 2025.
Adadin da ake hakowa a halin yanzu na kusa da ganga miliyan 1.4 a rana, sakamakon yawan satar mai, lalata bututun mai da kuma rashin saka jari.
Gwamnatin tarayya da ta jihohi na fatan samun karin kudin shiga daga man fetur domin aiwatar da kasafin kudin su.
Gwamnatin tarayya na da niyyar kashe N54.99tr a bana, yayin da jimillar kasafin kudin jihohi ya kai fiye da N25trn.
A jiya, danyen mai na Brent ya kusan $60 a ganga, inda Morgan Stanley ya shiga sahun sauran bankunan saka jari da suka rage hasashensu zuwa $62.5 a kan duk ganga.

Source: Twitter
Yadda farashin mai zai shafi kasafin kudi
Wannan hasashen na kawo barazana babba ga kasafin kudin Najeriya na N43bn wanda aka tsara bisa farashin $75 a ganga da kuma yawan hakar ganga miliyan 2.06 a rana.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Boko Haram ta kashe sojoji 4, ta kona dakin ajiyar makamai a Yobe
Bayan farashin mai ya fadi kasa da abin da kasafi ya tanada, Najeriya na fuskantar yiwuwar gibin kasafi har N30trn wanda ya ninka abin da aka tsara na N13trn.
A jiya, nau’in man Najeriya na Bonny Light, Forcados, da Qua Iboe suna cin kasuwa a kan kusan $60 a kowace ganga.
Wata majiya ta ce:
“Ina da tabbacin cewa masu siya na son biyan kudi fiye da kima ga nau’in man Najeriya, musamman ganin yadda bukatar kasuwa ke nan daram."
Kasafin kudi: Majalisa ta fadi dalilin kara N700bn
Kun ji cewa Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.
Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar ya bayyana dalilin yin ƙarin N700bn a kasafin kuɗin shekarar bana domin inganta rayuwar ƴan kasa.
Hon. Abubakar Kabiru Abubakar Bichi ya ce an yi ƙarin ne domin gudanar da wasu ayyuka masu matuƙar muhimmanci a cikin kasafin kudin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng