Hakeem Baba Ahmad Ya Shawarci Kwankwaso, Obi a kan Zaben 2027
- Hakeem Baba Ahmad ya ce kamata ya yi Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso su hakura da sake tsayawa takarar shugaban kasa
- Ya bayyana cewa sun yi kokari a baya, amma yanzu lokaci ya yi da za su ja daga gefe domin ba su da wani sabon abu da za su kara kawo wa Najeriya
- Baba-Ahmad ya nemi dukkan manyan ’yan siyasar da suka dade a fagen mulki, su ja gefe domin a ba matasa damar kawo canjin da kasa ke bukata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Dr. Hakeem Baba Ahmad, tsohon mashawararcin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a kan harkokin siyasa ya nusar da Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi a kan zabe mai zuwa.
Hakeem Baba Ahmad ya shawarci tsofaffin yan takarar shugaban kasa a jam'iyyun NNPP da LP da kada su tsaya takarar shugabancin Najeriya a 2027.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da Trust TV, Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa za su ja daga gefe su bar matasa su fito takara domin a gyara kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar Hakeem Baba-Ahmed ga Kwankwaso da Obi
Daily Post ta ruwaito cewa, Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa lokacin tsofaffin yan takarar ya wuce domin sun yi iya bakin kokarinsu, kuma babu wani sabon abu da za yi wa kasa.
A cewarsa:
"Peter Obi da Kwankwaso da shugaban kasa, Bola Tinubu da Atiku su ja daga gefe su bar matasa su fito takara. Sun ci zamaninsu, babu wani abin kirki da za su kara yiwa wa kasar nan."

Source: UGC
Ya kara da cewa:
"Muna ci gaba da fama da irin tsohon salon siyasa inda babu hakuri, kowa na son ya yi mulki da karfi da yaji.
"Amma idan sun hau mulki, babu kuzari ko karfin gwiwa da za su magance matsalolin kasa."
Hakeem Baba Ahmad ya yi tsokaci kan makomar Najeriya
Baba-Ahmed ya bayyana rashin amincewarsa da yadda shugabanni ke ci gaba da mulkin shekaru takwas, yana mai cewa hakan ba alheri ba ne ga Najeriya.
Ya ce:
"Ba na ganin makomar Najeriya za ta yi kyau a hannun tsofaffin 'yan siyasar da suka shafe shekaru 20 zuwa 30 suna jan ragamar mulki."
Ya ci gaba da cewa:
"Daya daga cikin abubuwan da ke bata siyasa a Najeriya shi ne wannan maganar dole sai an yi shekaru takwas a mulki. Wane ne ya ce dole ne? Lokacin da NEF ta gane cewa Buhari ya gaza, sai muka hada kai da wasu kungiyoyi a fadin Najeriya."
"Mun gana a nan Abuja muka sanar da kasa cewa ba mu yarda Buhari ya kara mulki ba. Ohanaeze, NEF, Afenifere da wasu kungiyoyi guda hudu ko biyar sun taru suka ce bai kamata a sake ba Buhari wa'adin mulki na biyu ba."
Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso
Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun fito daga bangarori daban-daban na Najeriya, kuma kowane daga cikinsu yana da salo na siyasa da ya bambanta da na ɗan uwansa.
Obi tsohon gwamnan jihar Anambra ne daga Kudu maso Gabas, wanda ya shahara da akidar rage kashe kudin gwamnati da gudanar da mulki cikin tsafta.
A zaben 2023, ya samu karbuwa sosai tsakanin matasa da masu neman sauyi, musamman a yankunan birane.
Ana kallon Obi a matsayin ɗan siyasa mai kishin gaskiya da neman canji, wanda ya fi dogaro da kafofin sada zumunta wajen samun goyon baya.
Kwankwaso, daga Arewa maso Yamma, tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma shi ya kafa tafiyar Kwankwasiyya.
Ya jima a cikin manyan jam’iyyun siyasar kasar, ciki har da PDP da APC, kafin daga bisani ya koma NNPP.
Siyasarsa na dogara ne da karfinsa na tallafa wa matasa da dalibai, musamman a Arewa ta fuskar ilimi.
Yana da kwarewa a tafiyar da gwamnati tare da tasiri ga shugabancin Kano, yana kuma da masu goyon baya da yawa a ciki da wajen jihar.
Ko da yake dukkansu sun yi tasiri a zaben 2023, akwai ra’ayin cewa yanzu lokaci ya yi da ya dace su ba matasa dama domin kawo sababbin dabaru a shugabancin Najeriya.
Hakeem Baba Ahmad ya dura a kan Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Hakeem Baba-Ahmed, tsohon hadimin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi kaca-kaca da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin siyasar ya ce babu wani shugaban kasa da ya mulki Najeriya da ya fi Buhari gazawa wajen kawo canjin da talakawa ke bukata.
Ya ce duk da cewa Arewa ce ta ba da goyon baya mai ƙarfi ga Buhari a shekarar 2015, ya gaza cika manyan alkawuran da ya ɗauka, ciki har da yaƙi da cin hanci da haɗa kan ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



