Kwamacala: Abin Kunya Ya Faru da Aka Kai Mata Kotu kan Zargin Auren Maza 2 a Kano

Kwamacala: Abin Kunya Ya Faru da Aka Kai Mata Kotu kan Zargin Auren Maza 2 a Kano

  • Wata mata mai suna Harira Muhammad ta gurfana a kotun Shari’a da ke Kano bisa zargin auren maza biyu lokaci guda ba tare da saki ba
  • Tsohon mijinta ya same ta da wani namiji a gadon aurensu, inda ta fara musanta auren kafin ta amsa daga baya
  • Kotun ta umurci ‘yan sanda su ci gaba da bincike tare da tsare Harira da sabon mijinta mai suna Bello Abdullahi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani abin al'ajabi da baƙin ciki ya faru a Kano bayan maka wata mata a kotu kan zargin auren maza biyu.

Matar ta gurfana a gaban Kotun Shari’a ta Sama da ke 'Post Office' a birnin Kano bisa zargin auren maza biyu lokaci guda.

An kai mata kotu kan zargin auren maza 2 a Kano
Mata ta yi martani da ake zarginta da auren maza 2 a Kano. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Daily Trust ne ya tabbatar da labarin faruwar lamarin a yau Talata 6 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan

Amarya ta kashe mijinta kwana 9 da ɗaura masu aure a Kano, an ji abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama ango kan zargin kisan amarya

A ƴan kwanakin nan, Legit Hausa ta ruwaito muku wani abin takaici da ya faru a jihar Jigawa tsakanin miji da matarsa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wani ango da abokansa bisa zargin hannu a mutuwar amaryarsa kwanaki bayan bikin aurensu.

Majiyoyi sun ce ango da wasu abokansa uku sun kutsa cikin ɗakin amarya da niyyar tilasta mata hulɗar aure, lamarin da ya janyo rasuwarta.

Rundunar ta umarci a mika binciken zuwa sashen CID na jihar domin zurfafa bincike da shirin gurfanar da su a gaban kotu.

Mata ta je kotu kan zargin auren maza 2

An ce Harira Muhammad Tudun Murtala da mijinta na fari, Sagiru Shuaibu T/Murtala, sun shafe watanni shida da aure amma suna zaune a gida daban-daban.

Majiyoyi sun ce lokacin da mijin ya ziyarce ta ne ya tarar da wani namiji a gadon aurensu.

Kara karanta wannan

Matashi ya kashe mahaifinsa bayan sassara wuyansa da adda a Jigawa

Nan take, bai yi wata-wata ba sai ya sanar da makwabta game da abin da ya gani na ban takaici.

Da ta bayyana a gaban kotu, matar ta fara musanta cewa tana auren mijinta na farko, amma daga baya ta janye bayan kotu ta bukaci rantsuwa.

An maka mata a kotu kan zargin auren maza 2 a Kano
Maza 2 sun auri mace 1 a Kano bisa rashin sani. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Martanin daya daga cikin mazajen matar

Mijin na biyu, Bello Abdullahi Yankaba, ya yi magana kan lamarin domin fayyace gaskiya.

Yankaba ya shaida wa kotu cewa dangin matar ne suka daura musu aure bayan ya biya sadaki N100,000.

Alkalin kotun, Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki, ya umurci ‘yan sanda su ci gaba da bincike tare da tsare su har zuwa ranar 16 ga Mayu.

Auren maza biyu kokaci guda

A cikin addinin Musulunci, addinin da galibin 'yan Arewacin Najeriya ke bi, aure yana daga cikin ibadu masu muhimmanci da ake kiyaye su da matuƙar tsarki.

Shari’ar Musulunci ta tanadi dokoki da ka’idoji game da halaccin aure da kuma batun saki.

Auren mace da mazaje biyu lokaci guda, wanda ake kira “tathniyya,” haramun ne a cikin Musulunci kuma laifi ne mai girma.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Boko Haram ta kashe sojoji 4, ta kona dakin ajiyar makamai a Yobe

Wannan hali yana karya ka’idar auren Musulunci, wanda ya tanadi cewa mace ta zauna da miji ɗaya kacal a kowane lokaci, sai dai idan an raba auren ta hanyar saki ko mutuwa sannan ta auri wani.

Idan mace ta yi aure yayin da tana auren wani, ana kallon wannan aikin a matsayin zina idan ba a samu saki ko cikakken mutuwar auren farko ba.

Wannan laifi na iya haifar da hukunci mai tsanani a gaban kotun Shari’a, ciki har da hukuncin haddi, wato hukuncin da aka kafa bisa nassoshi, kamar bulala ko har ma da jifa (rajm), gwargwadon yadda aka tabbatar da laifin da shaidu ko amsa aikatawa.

Musulunci ya tanadi wannan tsaurin doka ne don kare martabar aure da tabbatar da tsabta da shaidar haihuwa, da kuma kaucewa rikice-rikicen iyali da zubar da kimar darajar mata da mazaje.

Kano: Kotu ta daure matashi kan yunkurin kisa

Mun ba ku labarin cewa wata kotu a Kano ta fusata bayan an tabbatar da cewa wani matashi ya yi yunkurin hallaka mahaifinsa, saboda ya hana shi kudin batarwa.

Kotu ta yanke wa matashin hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari saboda yunƙurin kai wa mahaifinsa hari da almakashi a Fagge.

An ce matashin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya haɗa da ɗaukar makami ba bisa ƙa’ida ba da kuma barazanar kisa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.