Bayan Rahotonsa a kan Karuwar Talaucin Najeriya, Bankin Duniya Ya ba Tinubu Lakani
- Bankin Duniya ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da za su kare masu raunin cikin al'uma daga hauhawar farashi
- Rahoton Bankin ya ce lamarin hauhawar farashi yana kara dagula rayuwar talakawa, kuma babu wani ci gaba da za a iya samu a yaki da talauci
- Bankin Duniya ya fitar da alkaluma masu tayar da hankali, ya bayyana cewa mutane sama da miliyan 42 sun kara fadawa cikin talauci a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin Narayya da ta aiwatar da gyare-gyare da za su kare talakawan ‘yan Najeriya daga hauhawar farashin kaya da ake fuskanta a kasar.
Haka kuma, bankin ya bukaci gwamnati da habaka hanyoyin samun abin dogaro na halal ga daukacin al’ummar Najeriya ta hanyar samar da aikin yi domin rage talauci.

Source: Facebook
Channels TV ta ruwaito cewa Bankin Duniya ta bayyana haka a sabuwar rahotonsa a kan talauci na watan Afrilu 2025 da aka fitar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Akwai karuwar talauci a Najeriya,” Bankin Duniya
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Bankin Duniya ya bayyana cewa karin ‘yan Najeriya za su fada cikin talauci cikin shekaru biyar masu zuwa.
Bankin ya danganta hakan da rashin karfi na tsarin tattalin arzikin Najeriya, dogaro da kudin shiga na man fetur, da kuma tabarbarewar tsarin mulki a kasa.
A wani yunkuri na rage radadin hauhawar farashin da sauye-sauyen gwamnati suka jawo wa marasa karfi, gwamnati ta kaddamar da shirin raba tallafin kudi na wucin gadi ga gidaje miliyan 15.
Sai dai Bankin Duniya ya ce aiwatar da shirin na tafiyar hawainiya, wanda ya sa ba a samu nasarar da aka si cimmawa ba.
'An samu hauhawar farashi a Najeriya' - Bankin duniya
Rahoton Bankin Duniya ya ce hauhawar farashin kaya na shekara-shekara a Najeriya ya tashi kadan zuwa 24.23% a watan Maris 2025, daga 23.18% a watan da ya gabata.
Farashin kayan abinci, wanda a nan ne aka fi samun hauhawar farashi ya dan sassauto 21.79% daga 23.51% a watan da ya gabata.

Source: Facebook
Bankin ta bayyana cewa:
"Tun daga shekarar 2018/19, karin mutane miliyan 42 sun fada cikin talauci, wanda hakan ke nuna cewa fiye da rabin ‘yan Najeriya (54%) ana hasashen za su rayu cikin talauci a shekarar 2024, bisa kiyasin Bankin Duniya.”
Bankin Duniya ta bukaci amfani da kudin gyaran fetur wajen karfafa tsare-tsaren tallafi
Bankin Duniya ya yabi Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bankin Duniya ya bukaci gwamnati ta dauki matakin raba dukiyar da ake samu daga arzikin man fetur ga talakawa domin rage radadin talauci.
Mataimakin shugaban Bankin Duniya mai kula da lamurran tattalin arziki na duniya, Indermit Gill, shi ne ya bayyana hakan, inda ya jaddada cewa mafi yawan 'yan Najeriya na fama da talauci.
Mista Gill ya kara da kara bayyana damuwarsa kan yadda hauhawar farashi ke kara jefa rayuwar jama'a cikin matsi, musamman wadanda ke cikin kashi mafi rauni na al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

