'Yan Bindiga Sun Gwabza Fada da 'Yan Sa Kai, an Samu Asarar Rayuka
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a yayin harin da suka kai
- Ƴan bindigan sun kuma yi wa wasu ƴan sa-kai masu yin aikin sintiri kwanton ɓauna a cikin daji, wanda hakan ya jawo asarar rayuka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu satar shanu ne sun kashe sama da mutane 10, ciki har da ƴan sa-kai, a ƙauyen Mansur da ke yankin Gwana, a ƙaramar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi.
Haka kuma, ƴan bindigan sun sace shanu da tumaki daga ƙauyen Mansur da wasu ƙauyuka da ke makwabtaka da yankin.

Source: Original
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƴan sa-kan sun faɗa tarkon ƴan bindigan ne yayin da suke sintiri a dajin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun tabbatar da harin ƴan bindiga
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 5 ga. watan Mayun 2025.
CSP Ahmed Wakil ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 9:40 na dare.
Ya ce rundunar ta karɓi rahoto daga ofishin ƴan sanda na Alkaleri kan wani harin ƴan bindiga da ya faru a ranar da misalin ƙarfe 5:40 na yamma.
“A lokacin da wata tawagar mafarauta daga yankin Duguri da Gwana suke gudanar da sintiri a kan hanyar Duguri, Mansur da dajin Madam da ke kan iyaka tsakanin Bauchi da Plateau, sun faɗa tarkon kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka shirya."
"Wannan artabu ya haddasa rasa rayuka da dama daga ɓangarorin biyu, ciki har da ƴan sa-kai da kuma ƴan bindigan da suka kai harin."
- CSP Ahmed Wakil
Kakakin rundunar ya ce an tura tawagar sintiri zuwa wajen da lamarin ya faru, inda suka ceto gawarwakin waɗanda aka kashe.
CSP Wakil ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa waɗanda suka mutu sun haɗa da ƴan sa-kai da kuma fararen hula daga ƙauyen Sabuwar Sara, wadanda aka harbe su yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin.

Source: Twitter
Kwamishinan ƴan sanda ya kai ziyara
Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Sani Aliyu, ya kai ziyara zuwa wurin da lamarin ya faru domin duba halin da ake ciki.
Ƴan bindiga sun taba kai makamancin wannan hari shekaru da suka wuce a ƙauyen Mansur da wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da shi, inda suka kashe mutane da ƙona gidaje.
Ƴan bindiga sun kashe mafarauta a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindigan sun hallaka mafarauta a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ƴan bindiga sun hallaka mafarautan ne a ƙaramar hukumar Tangaza yayin wani musayar wuta da suka yi.
Harin na ƴan bindigan ya ƙara nuna matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

