Tashin Hankali: Boko Haram Ta Kashe Sojoji 4, Ta Kona Dakin Ajiyar Makamai a Yobe

Tashin Hankali: Boko Haram Ta Kashe Sojoji 4, Ta Kona Dakin Ajiyar Makamai a Yobe

  • Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan sansanin sojoji a Buni Yadi, inda suka kashe sojoji hudu tare da kona kayan yaki
  • Harin ya auku kasa da sa’o’i 24 bayan taron gwamnonin Arewa maso Gabas da suka tattauna hanyoyin yaki da ta’addanci a Damaturu
  • An ce maharan sun kutsa sansani nda misalin karfe 2:00 na safe, suka kwashe makamai, suka kona bindigogi, motoci, da MRAP biyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yobe - Wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne sun kai mummunan hari kan rundunar sojojin Nageria ta 27 da ke jihar Yobe.

An ce 'yan ta'addan sun hallaka akalla sojoji hudu tare da lalata dumbin kayan aikin sojin a garin Buni Yadi, karamar hukumar Gujba ta jihar.

Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji4 sun lalata makamai a Buni Yadi, jihar Yobe
Dakarun sojojin Najeriya yayin da suke rangadi a cikin daji. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Boko Haram sun farmaki sojoji a Buni Yadi

Kara karanta wannan

An gano illar rikicin filaye a Najeriya bayan an salwantar da rayuka kusan 2000

Wannan harin ya faru kasa da awanni 24 bayan da kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas ta gana a Damaturu, babban birnin jihar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce gwamnonin sun amince da wasu hanyoyi da dama na magance matsalar 'yan tada kayar baya da suka addabi yankin.

An rahoto cewa garin Buni Yadi ta na da tazarar kilomita 65 daga birnin Damaturu, kuma ita ce mahaifar gwamnan jihar, Mai Mala Buni.

Wani jami'in tsaro da ya tsira daga harin ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun afka musu da misalin karfe 2:00 na safiyar Asabar.

'Muna kan fafatawa da ISWAP' - Sojoji

Ya ce 'yan ta'addan sun fatattaki sojojin daga sansanin kuma sun kona dukkanin kayan aikin da aka ajiye a wurin.

Ya kara da cewa:

"Sun kutsa kai cikin dakin ajiyar makamai, sun kwashi na kwasa sannan suka kona sauran; sun kona manyan bindigogi, motocin yaki guda biyar kirar MRAP, da motocin daukar makamai masu linzami, da kuma motocin Hilux fiye da 20."

A ranar Asabar, hedkwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da faruwar harin a shafinta na Facebook, amma ba ta bayar da cikakkun bayanai kan barnar da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Fada ya ɓarke tsakanin ƴan sanda da dakarun Amotekun, an yi harbe harben bindiga

A sanarwar da ta wallafa, rundunar sojin ta ce:

"A halin yanzu dai sojojin Operation Hadin Kai na cikin wani kazamin fada da 'yan ISWAP a Buni Gari, jihar Yobe. Za a bayar da cikakkun bayanai daga baya."

An kashe sojoji 4, an lalata makamai

Sai dai wani soja da ya tsira daga harin ya ce 'yan ta'addan sun shigo yankin daga Yamma, inda suka rika jefa masu bama-bamai tare da yin harbi ba kakkautawa.

A cewar sojan:

"Bama-bamai da harbe-harben sun yi mana yawa, amma mun tsaya tsayin daka har zuwa lokacin da suka fi karfinmu. Sun lalata yawancin kayan yaki a lokacin da muka kara da su."

Ya kuma kara da cewa:

"Tabbas, mun rasa mutanenmu hudu, kamar yadda suma suka samu asarar mutanensu a wannan kazamin fadan da ya dauki awanni ana yi."

Boko Haram sun farmaki sansanin sojoji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yayin da ake tsammanin samun nasara kan yaki da rashin tsaro, 'yan ta'addan Boko Haram sun sake kai jerin hare-hare kan sansanonin sojoji a Borno.

Kara karanta wannan

Abu ya yi zafi: Akwai yiwuwar ta'adi, kwamandojin ƴan bindiga sun gana a Zamfara

Maharan sun kai wadannan hare-hare ne a sansanonin sojojin da ke cikin kananan hukumomin Damboa da Gambaru Ngala a ranar Litinin, 24 ga Maris, 2025.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana damuwarsa game da yawaitar hare-haren 'yan Boko Haram a fadin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com